BBC Hausa of Thursday, 22 April 2021

Source: BBC

Mason ya fara jan ragamar Tottenham da kafar dama

Dan kwallon Tottenham Mason tare da dan uwa Son Dan kwallon Tottenham Mason tare da dan uwa Son

Tottenham ta yi nasarar doke Southampton da ci 2-1 a kwantan wasan mako na 29 a gasar Premier da suka kara ranar Laraba.

Southampton wadda Leicester City ta yi waje da ita a karawar daf da karshe a FA Cup, ita ce ta fara cin kwallo ta hannun Danny Ings, saura minti 15 su tafi hutu.

Daga baya Tottenham ta farke ta hannun Gareth Bale, sannan Heung-min Son ya ci na biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga kuma daf a tashi karawar.

Wannan ne wasan farko da kocin rikon kwarya tsohon dan kwallon kungiyar, Ryan Mason ya fara jan ragama, tun bayan da ya maye gurbin Jose Mourinho da aka kora ranar Litinin.

Mason mai shekara 29 shi ne matashin kocin Premier League mai karancin shekaru a gasar ta Ingila a bana.

Tottenham tana daga cikin kungiyoyin Ingila shida da suka fice daga gasar European Super League da aka kirkira don kungiyoyi 12 su fafata a tsakaninsu.

Bayan Tottenham wadan da suka fice daga gasar sun hada da Arsenal da Liverpool da Chelsea da Manchester United da kuma Manchester City.

Da wannan sakamakon Tottenham ta koma ta shida a teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da ta hudun farko a saman teburin gasar bana.

Mason zai kuma ja ragamar Tottenham a wasan karshe a Caraboa Cup da Manchester City a Wembley ranar 25 ga watan Afirilu.