BBC Hausa of Monday, 12 April 2021

Source: BBC

Matakan da ake bi don duban watan azumi a Najeriya

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III

Kwamitin duban wata na Najeriya ya umarci ƴan kasar da su fara duban jaririn watan azumin Ramadan daga ranar Litinin.

Shugaban Kwamitin, Farfesa Sambo Wali Wazirin Sokoto ya shaida wa BBC cewa, Litinin ce 29 ga watan Sha'aban kuma idan ba a gan shi ba da yamamcin Litinin, to za a ci gaba da duban watan zuwa Talata.

"Idan kuma ba a gan shi ba a ranar Talata, to kai tsaye Laraba za ta kasance 1 ga watan azumin Ramadana," in ji Waziri.

Farfesa Sambo ya ce babu yadda za a yi kwamitinsu ya saɓa da ka'idar duban wata da addinin musulunci ya gindaya saɓanin yadda wasu jama'a ke zato.

A cewarsa, kwamiti na amfani da Hadisin Manzon Allah (SAW) "ku yi azumi idan kun ga wata, ku ajiye idan kun ga wata - idan ba ku samu ganinsa ba kila saboda hadari to ku cika Talatin."

Ya yi watsi da zargin cewa suna tafiya tare da Saudiyya inda ya ce lokacin azumi kawai Saudiya ke duban wata saɓanin kwamitinsu da ko wane wata ke fita duban sabon wata.

Matakan da ake bi

Kwamitin duban wata a Najeriya ya ce duk ƙarshen wata wakilan kwamitin suna zama kuma a bayar da sanarwa cewa 29 ga wata jama'a su fita duban sabon wata.

Kwamiti yana aika wa dukkanin yankunan Najeriya cewa idan an ga wata a yi sauri a faɗawa mai alfarma Sarkin Musulmi

Idan mutum shi kaɗai ya ga wata zai sanar da Hakimi zuwa ga Uban Kasa wanda shi kuma zai sanar da Sarkin Musulmi.

Daga nan za a jira a fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi har a samu labarin ganin wata a faɗin Najeriya ko kasashen waje.

Za a sanar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi cewa an ga wata saboda haka gobe 1 ga sabon wata - idan ba a ganshi ba kuma gobe za ta kasance 30 ga wata.

Idan sarkin musulmi ya gamsu da bayanan da aka ba shi bayan ya tuntuɓi sarakuna na jihohin arewa da na yamma domin tabbatar masa da ganin watan.

"Ta haka ake samun labarin an ga wata ko ba a ganshi ba," in ji Wazirin Sokoto Farfesa Sambo Wali, shugaban kwamitin ganin wata a Najeriya.

Ya kuma ce Kwamitin ganin wata kan zauna da waɗanda suka ga wata, domin a yi masu tambayoyi cewar - ya kuka ga wata? Ina kuka gan shi?

Ya ce kwamitin kan kiyaye lokaci da kuma yadda aka ga wata, da ɓangaren da aka ganshi domin a cewarsa: "Mafadar wata ya bambanta da yanayi - lokacin hunturu ya bambanta da na bazara da kuma na damina.