BBC Hausa of Wednesday, 10 March 2021

Source: BBC

Matasa 12 sun nutse a cikin teku a Ghana

Ma'aikatan ceto sun gano gawawwakin yara 12 da suka nutse Ma'aikatan ceto sun gano gawawwakin yara 12 da suka nutse

Ma'aikatan ceto sun gano gawawwakin yara 12 da suka nutse kusa da bakin teku da ya yi fice a kudancin Ghana.

Suna cikin yara masu shekaru 14 da 17 da suka je ninkaya a ranar Lahadi a garin Apam.

Iyaye da mazauna garin sun taru a gaban tekun domin jin labarin wadanda suka bata.

"Na neme shi a yammacin Lahadi amma ban same shi ba, ban iya bacci ba amma daga baya na ji cewa wasu yara sun nuste kuma an tsamo gawawwakinsu. Don haka na wuce can inda na same shi a cikinsu"" in ji wani mahifi.

Wata mata ta ce an gano wasu gawawwaki a ranar Litinin yayin da wasu a ranar Talata.

An rufe bakin teku a Ghana domin dakile bazuwar annobar korona sai dai an ce yaran sun bi wata hanya ne domin kada a hanasu zuwa wurin.

An ajiye gawawwakin mamatan a wani asibiti da ke garin na Apam.

Wani jami'i a hukumar yawon bude ta kasar ya ce abu ne mai wuya 'yan sanda su iya gadin gabar tekun kasar mai tsawon kilomita 540

Yin iyo a duk wani bangare na bakin tekun Ghana na da hatsari sosai saboda ana samun ruwa da ke zuwa da karfin gaske, sai dai akasarin bakin tekun da ke kasar basu da jami'an tsaro ko tutocin da za su ankarar da mutane game da hadarin da ke wurin.