Wata matashiyar Kano a arewacin Najeriya da ta ƙera wata manhajar da za ta dinga bayar da rahotanni kan fyaɗe ya ja hankalin ƴan Najeriya a kafofin sada zumuna musamman Twitter.
Saadat Aliyu ƴar asalin jihar Kano ta samar da sabuwar manhaja ce 'Helpio App' mai bayar da bayanai kan cin zarafin mata wacce ta ƙaddamar a rumbun manhaja na wayoyin android wato Play Store a 2020.
Saadat ita ce shugabar kamfanin Shamrock Innovation mai ƙirƙire-ƙirƙiren fasaha kuma mai fafutikar ci gaban mata a fannin ƙirƙira.
Yadda aka gabatar da matashiyar a kanun labaran wasu jaridun ƙasar a matsayin 'Kano Lady' wato budurwa ƴar Kano shi ya ja hankalin ƴan Najeriya a kafofin sada zumuna musamman a Twitter.
"Kano Lady" na cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a shafin na Twitter tun daga ranar Litinin zuwa Talata inda kusan mutum 15,000 suka yi tsokaci akai.
Duk da ba kasafai akan samu mata ba a fagen ƙirƙirar fasaha a Najeriya musamman arewacin ƙasar ba, amma wasu na ganin ta cancanci yabo kuma ya dace a kira ta da sunanta na yanka.
Yawanci dai kafafen yaɗa labarai kan alaƙanta mutum da sunan garinsa musamman wanda ba sananne ba.
Me ake cewa?
Abin da yawanci mutane suka fi tattaunawa shi ne rashin kiran matashiyar da sunanta na asali.
Suna ganin irin fasahar da ta samar bai dace a mayar da hankali ga garin da ta fito ba.