BBC Hausa of Saturday, 24 April 2021

Source: BBC

Mazauna ƙauyuka sun kashe ƴan fashi 10 da suka kai musu hari a Zamfara

Ƴan fashin a kalla 10 ne suka mutu a cikin bata kashin da suka yi da 'yan banga Ƴan fashin a kalla 10 ne suka mutu a cikin bata kashin da suka yi da 'yan banga

Bayanai daga jihar Zamfara a arewacin Najeriya na cewa wasu 'yan fashin daji sun kwashi kashinsu a hannu a daren Juma'a lokacin da suke ƙoƙarin farmaki kan wasu ƙauyuka biyu da ke kusa da babban birnin jihar.

Ƴan fashin a kalla 10 ne suka mutu a cikin bata kashin da suka yi da 'yan banga a ƙauyukan Kwaya da kuma Kura da ke ƙaramar hukumar Gusau.

Wannan na zuwa ne yayin da mazauna ƙauyukan nan shida da suka kai wa farmaki a shekaran jiya ke cewa adadin wadanda suka mutu yanzu ya kai 80.

A cewar mazauna yankin 'yan fashin dajin sun gamu da gamon nasu ne a wani artabu da 'yan banga a ƙauyukan Kwaya da kuma Kura lokacin da suka yi yunkuri afka musu da tsakar daren jiya.

Wani ɗan sa kai da aka yi fafatawar da shi, ya ce turjiyar da suka nuna da kuma ɗaukin da aka kai daga maƙwabtan ƙauyuka ne suka taimaka musu suka fatattaki maharan tare da hallaka 10 daga cikinsu.

Ya ce "Jiya da misalin sha biyu da 'yan kai na dare, da yake ba barci muke ba muna gadi saboda halin da muke ciki. Sai 'yan wancan garin suka kira mu suka ce mukai musu ɗauki ga ƴan fashin sun zo.

"Da haka muka je dauke da bindigoginmu na toka duk da cewa su suna dauke ne da AK47 amma a haka muka ci galaba a kansu har muka kashe mutum 10.

"Da suka ga haka sai suka gudu, ba su samu nasarar shiga garuruwan ba. Ko kaza ba su ɗauka," a cewarsa.

Amma ya ce a yanzu suna buƙatar jami'an tsaro, "yanzu haka akwai mata da suka gudo daga ƙauyukan sun fi 3,000 don ƴan fashin sun ce sai sun dawo. don haka dole gwamnati ta taimaka ta turo mana tsaro."

Mutumin ya ce gawarwakin ƴan fashin da suka kashe ɗin suna nan jibge bakin waɗannan ƙauyukan. "Na gansu da idanuna sosai."

Wannan artabun ya zo ne yayin da mazauna ƙauyukan nan shidda na yankin Magami da suka fuskacin hare-hare ranar Laraba ke cewa har yanzu suna ci gaba da zaƙulo karin gawarwakin wadanda 'yan fashin suka halaka daga daji.

Wata majiyar tsaro a jihar ta Zamfara dai ta tabbatar wa da BBC duka lamurran biyu, wato kashe 'yan fashin daji 10 da kuma karuwar adadin wadanda suka mutu daga hare-haren na shekaran jiya zuwa tamanin.

Ita ma gwamnatin jihar ta Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin na Magami a cikin wata sanarwa, tare da yin Allah wadai da abin da ta kira tsabagen aikin ta'addaci kan bayin Allah da ke neman abin kai wa baka.

Sai dai ba ta ce komai ba kan adadin wadanda aka karkashen.


Rufe kasuwanni

Sanarwar da ma'aikatar watsa labaran jihar ta fitari ta ce a wani mataki na maganin wannan matsalar, gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe wasu kasuwanni hudu a sassa daban-daban na jihar.

Kasuwannin kuwa sune na garuruwan Magami da Wanke a karamar hukumar Gusau, da ta garin Dansadau a karamar hukumar Maru, da kuma ta Dauran a karamar hukumar Zurmi.

Sanarwar ta kuma ce an bai wa jami'an tsaro umarnin su tabbatar da ana bin doka kamar yadda ya kamata.

An kuma ba su umarnin su yi aiki babu sani babu sabo ga duk wanda suka kama ya karya doka a yankin da kasuwannin suke.

"Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin shugabancin Gwamna Bello Mohammed Matawalle ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai a ranar Laraba," in ji sanarwar.