Paris St Germain ta yi nasarar doke Saint Etienne da ci 3-2 a wasan mako na 33 a gasar Ligue 1 ta Faransa da suka fafata ranar Lahadi.
Saint Etienne ce ta fara cin kwallo ta hannun Denis Bouanga saura minti 13 a tashi daga wasan.
Sai dai minti biyu tsakani PSG ta farke ta hannun Kylian Mbappe, sannan ya kara na biyu saura minti 11 a tashi daga fafatawar.
A minti na 90 ne St Etienne ta farke wasa ya koma 2-2, nan da nan PSG ta kara na uku ta hannun Mauro Icardi da hakan ya sa ta hada maki ukun da take bukata.
Kwallo biyun da Mbappe ya ci a ranar Lahadi ya ci gaba da zama na daya a yawan zura kwallaye a raga a gasar ta Faransa mai 23 a raga a wasa 28 da ya yi a bana.
Da wannan sakamakon PSG tana ta biyu a teburin Ligue 1 da tazarar maki daya tsakaninta da Lille mai jan ragama mai maki 70.
PSG ta kai karawar daf da karshe a gasar Champions League a bana, za kuma ta fafata da Manchester City a wasan zagayen gaba.
Kungiyar ta Faransa wadda ba ta taba lashe Champions League ba, ta kai wasan karshe a bara, inda Bayern Munich ta yi nasara da ci 1-0 ta kuma ci kofi na shida jumulla.
Jerin wadan da ke kan gaba a cin kwallaye a Ligue 1 ta bana:
- Kylian Mbappe PSG 23
- Wissam Ben Yedder Monaco 17
- Memphis Depay Lyon 16
- Boulaye Dia Stade Reims14
- Kevin Volland AS Monaco FC13
- Karl Toko Ekambi Lyon 12
- Moise Kean PSG 12
- Ludovic Ajorque RC Strasbourg 12
- Andy Delort HSC Montpellier 12
- Amine Gouiri OGC Nice 11
- Terem Moffi Lorient 11
- Ui-jo Hwang Bordeaux 11