BBC Hausa of Saturday, 17 April 2021

Source: BBC

Me ya sa muke kururuwa idan muna cikin annashuwa?

Masana sunyi bayani me ya sa ake kururuwa idan muna cikin annashuwa Masana sunyi bayani me ya sa ake kururuwa idan muna cikin annashuwa

"Na cika da tsoro, amma ba na son na gaza yi, don haka na kasance a koda yaushe idanuna a rufe. Ina fada a raina cewa ba zan sake yin irin wannan ba."

A shekaru takwas, Alejandra Mendoza ta yi wani alwashi. Amma da dadewa ba ta saba alkawarin da ta yi ba. Ba sau daya kawai ba, amma sau da dama.

Tsananin firgitar da ta yi a hawa lilonta na farko ne ya sa hakan ya zamar mata wani abin da ta fi kaunar yi, na juyawa, da lulawa sama sullowa zuwa kasa wanda ake gudanarwa a dandalin shakatawa ne - kururuwa na ciki.

Amma a yayin da wasan dandalin shakawata mafi girma a Amurka ke shirin sake budewa a farkon wannan watan, an umarci masu hawa lilon a jihar California su rage annashuwar da suke da ita su rage yawan kururuwa don kauce wa yada kwayar cutar korona.

Amma shin za a iya hana yin kururuwa kuwa, me ya sa muke yi idan aka ce bai kamata mu yi annashuwa ba?

Menene kururuwa?

Ana kasa yin kururuwa a matsayin "babu magana dungurungum" nuna alama da baki, kamar yadda farfesan halayyar dan adama na Kwalejin Emory College, Harold Gouzoules ya bayyana.

"Ihu na nufin kana daga muryarka, amma kana ci gaba da magana," ya ce.

"Kururuwa fitar da sauti ne na daban, suna da dangantaka ta yanayi; Sukan fara da sauti mai karfi kuma su ci gaba da karar sautin da kan kai tsawon dakikoki.

"Don haka yakan kasance na kankanin lokaci, mai karfi, mai amo, mai cin dogon zango.''

Me ya sa muke kururuwa?

"Kururuwa ta samo asali ne daga wata hanya ta zaburar da dabba mai farauta, tare da ba da wata karamar dama na tserewa," in ji Farfesa Gouzoules.

Kamar yadda kaka da kakanninmu suka bayyana, kururuwa na zama wani kiran neman agaji daga iyalai mafi kusa.

"Amma muddin kururuwa za ta kasance wata madogara ta murya wajen yin hakan, dole ka iya gane muryar 'yar uwarka ko dan uwanka ko kuma wani daban," a cewar Fafesa Gouzoules.

"Yin kururuwa a tsakanin wadannan rukunin mutane kan nuna wa abokanka yadda kake idan ka yi kururuwa.

"Ba sai ka jira rayuwarka ta kasance cikin hadari ba kafin ka koya wa 'yayanka yadda sautin kururuwarka yake ba."

Me ke faruwa a kan lilon?

Yawancin masu tsananin son hawa lilo ba su gamsu da batun karuwa da ci gaban da aka samu ba, amma sun fi amincewa da ci gaba a fannin nishadi da annashuwa.

Amma kuma, kamar yadda farfesa Gouzoules ya bayyana, duka biyun na da alaka.

"Kwakwalenmu na samar mana da jin dadi da annashuwa da ke bayar da gudumawa a bangaren rayuwarmu," ya ce.

"Muna cikin wani zamani na ci gaba, kuma ga akasarinmu ba sai mun yi kururuwa ba a kullum, amma shakka babu ba ina nufin ba ma fuskantar barazana daga lokaci zuwa lokaci ba.

"Kuma me yiwuwa za mu yi kururuwa kamar yadda muke yi a lokacin kaka da kakanni. Barazanar za ta fi zama a koda yaushe me yiwuwa, amma dai kururuwa na da amfani ne a fannin yadda mu ke fama da rayuwarmu ta duniya."

Ga mutanen wannan zamani, zabi daya shi ne na lilo da kuma sauran dandalin shakatawa.

"Zuciyarka tana bugawa, jininka ya hau, don haka kana fama da firgici a kan lilo duk da cewa ka san babu wani hadari," in ji Gouzoules.

"Akwai dimaucewa kuma kururuwa na sa ka rage damuwa."

Hakan ya nuna wani kamar iri su Alejandra, cewa kururuwa a kan lilon na kasancewa kamar kana jin tsoro, amma kuma kana cikin annashuwa ne.

"Zan iya cewa kamar wni rage damuwa ne, saboda kana mancewa da komai ne, kana kawai cikin wani yanayi,'' mai shekaru 25 daga Ecudor ya kara bayyanawa.

Wata mai rubuce-rubuce a shafin intanet kan harkokin sufuri Dymphe Mensink ta amince , kuma ta ce tun tanakarama take hawa lilon.

"A koda yaushe nakan so ganin wuraren shakatawa a cikin birane saboda shi ne abin yi mafi annashuwa a ra'ayina," ta ce.

Mai shekaru 23 da ke zaune a birnin Amsterdam ta ce: "Lokacin akwa dogon layi, kana ganin tankwarewar lilon sai da dama, kana za ka rika godiyar Ubangiji cewa ba ka cikin lilon, da hakan kan kara zama da ban tsoro.

"Kana kuma muddin ina ciki, wasu lokuta ka kan lula can sama a hankali ne, sai ka dan fara jin tsoro, amma idan na fado na kan ji farin ciki in ji ina son yin kururuwa."

Ita kuwa Dymphe cewa ta yi wannan fitar da sauti "na kan ji wata gamsuwa" wacce ke sa na bayyana yadda nake ji."

"Ina ga wani abu ne da ba za ka ji ba in a haka nan ne."

"Na kan ji karin farin ciki lokacin da na yi kururuwa, ko shakka babu abin gamsarwa ne a gare ni."

Aki Hayashi, da aka haifa ya kuma girma a birnin Uraysu, inda shahararren wurin shakatawar nan na Disneyland da ke Tokyo, ya ce ya dade da matukar kaunar hawa lilon a rayuwarsa.

A cewarsa: "Ba zan taba jin dadin rayuwata ba tare da hawa lilon nan ba."

Mai shekaru 27 shi ne shugaban kungiyar masu hawa lilon na kasar Japan, wadanda ke zuwa wuraren shakatawar tare.

Ya ce kururuwa wani martani ne da ya kan iya nuna wa, bayan da ya hau kimanin irin wannan lilon 350 fadin duniya.

"Idan ina kan lilon, nakan yi kamar bana jin dadinsa, saboda kowa na kallona a lokacin da nake kururuwa."

"Amma taron masu hawa lilon ya kan zama kamar wani biki, mutane kan yi ta kururuwa suna ihu tare.

"Yakan saka ni farin ciki idan muna kururuwa kuma yana sauka.''

Farfesa Gouzoules ya ce kokarin kauce wa yin kururuwa zai iya faruwa, amma kuma kalubale ne mai wahala ga wasu daidaikun mutane.

''Wasu mutane za su iya daurewa, amma wasu ba za su iya ba,'' ya ce.