Ƴan Najeriya sun jima suna nuna damuwa kan rashin tsari da ingantaccen kayayyakin kashe gobara a ƙasar, sai dai a yanzu damuwar ta koma kan ƙaruwar da ake samu na tashin gobara a kasuwannin a wasu jihohin da dama da ke jawo asarar ɗumbin dukiyoyi da ƙadarori.
Masana dai na ganin bai kamata a ce a ko da yaushe ana yawaita samun irin wannan gobarar ba a ƙasar da ake ganin ita ce kan gaba wajen yawan al'umma da ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka.
Kusan kowacce jiha ta fuskanci mummunan ibtila'in gobara a kasuwanninta. Kama daga Jihar Legas zuwa Maiduguri da Kano da Onitsha da Sokoto, labarin a ko da yaushe iri guda ne - asarar ɗmbin dukiyoyi da ƙadarori wani lokaci har da rasa rai.
Karuwar irin wannan gobara na sake hadasa damuwa musamman tsakanin ƴan kasuwa da ke asarar arziki mai tarin yawa. Irin wannan asarar ana jimawa ba a manta ba kuma tasirin na ɗaukar tsawon shekaru.
- Gobarar da ta tashi a babbar kasuwar Sokoto 'ta laƙume miliyoyin naira' Kalli hotunan gobarar kasuwar Balogun a Legas
Ko kafin wannan lokaci an samu irin wannan gobarar a babbar kasuwar Sokoto, lamarin da ya janyo asarar dukiya ta miliyoyin naira a watan Janairun da ya gabata.
Sannan a shekarun baya an samu irin wannan munanan gobarar a kasuwanni irin Balogun ta Legas da Sango Plank ta Ibadan da kasuwar Ochanja ta Onitsha da Kwari da Sabon Gari a Kano.
Akwai wadda ta auku a 2019 a Kano a kasuwanni Yan Katako da Kofar Ruwa da Kurmin Yan-nama.
Me ke jawo gobara a kasuwanni?
Abin takaici ne ganin yayinda wasu ƙasashen duniya ke fama da annoba ko iftila'i da dama sakamakon matsalolin sauyin yanayi, a Najeriya labarin daban yake saboda galibin wadannan gobarar laifin mutane ne, kamar yadda Muhammad Mustapha Rilawan tsohon shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya shaida mana.
'Ga wasu dalilai da ke jawo gobara'
- Rashin tsafta Rashin wutan lantarki Rashin tsari da hanya Rashin tsaro Rashin tashoshin kashe gobara a kasuwanni Cunkoso
Hanyoyin magance matsalar gobara a kasuwanni
Malam Mustapha ya ce, galibin gobarar da ake gani a kasuwanni a sassa da dama na Najeriya ana iya hana afkuwarta idan gwamnati da ƴan kasuwa za su iya haɗa kai wajen daukar matakan kariya.Misali, matsalar wutar lantarki, wadda galibi ake alaƙanta tashin gobara da ita, ana iya shawo kanta idan za a wadatar da mutane da ƴan kasuwa da wutar lantarki domin hakan zai taƙaita amfani da janereto ko batira da ke hadasa gobara, in ji Malam Mustapha.
Sannan ya ƙara da cewa, akwai bukatar inganta tsaro a kasuwanni musamman da dadare. A fitar da tsarin lokacin tashi da buɗe kasuwanni. Ko da yake akwai kasuwanni da ke da wannan tsarin, in ji shi.
"Akwai bukatar samar da hanyoyin da galibi ke haifar da cikas wajen kai ɗaukin gaggawa idan an samu tashin gobara.
Kazalika kuma bukatar tilasta tsafta da yawan shara da hana kwanan kasuwa da samar da tashoshin kashe gobara kuma kowanne shago ya mallaki abin kashe gobara".
'Sauya tsarin kasuwanni'
Malam Mustapha, ya ce muddin gwamnati ba ta tashi tsaye wajen inganta tsarin yadda ake harkoki a kasuwanni ba, da bijiro da doka mai karfi ta tsaro, da tilasta dabi'un kariya, to matsalar gobara a kasuwannin Najeriya ba wadda za a iya kawo ƙarshenta ba ne a nan kusa.
Sannan akwai buƙatar samar da kasuwanni irin na zamani a kowacce ƙaramar hukuma. Wannan nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnatoci jihohi da tarayya muddin an shirya ganin sauyi.
Akwai kuma buƙatar wayar da kawunan ƴan kasuwa kan bukatar taka tsan-tsan, na kuma hana shan sigari a cikin kasuwanni. Masu sana'ar abinci ko girki a kasuwa ma a dinga sanya musu ido.