Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce 'yan jarida "suna yunkurin wallafa abubuwan da ban taba na fada ba".
Ya bayyana haka ne a hirar da ya yi bayan wasan da suka yi nasara da ci 1-0 kan Chelsea.
Arteta ya ce gabanin wasan ba dukkan 'yan wasansa ne suke da kuzari iri daya ba sai dai wasu 'yan jarida sun ce wannan kalamin tamkar nuna rashin kwarin gwiwa ne kan 'yan wasansa.
Ya shaida wa BBC Radio 5 Live cewa: "Ba zan yarda wani ya je ya fadi abin da ba ni na fada ba.
"Idan abu ne da ya shafi 'yan wasana, zai kashe musu gwiwa."
Ya kara da cewa: "Za ['yan jarida] su iya bayyana ra'ayinsu daga waje, ba matsala game da hakan, amma ba za su iya yunkurin karya mu ba."
Emile Smith Rowe neya zura kwallon guda daya a Stamford Bridge lamarin da ya bai wa Gunners karin dama yayin da Chelsea ta sha kaye na uku a karkashin jagorancin Thomas Tuchel.
Yanzu Arsenal tana mataki na takwas a teburin gasar Firimiya bayan cin wasa uku a jere, sai dai fatansu na samu gurbin zuwa gasar Zakarun Turai ya zo karshe a makon jiya.