BBC Hausa of Friday, 9 April 2021

Source: BBC

Mohamed Bazoum ya nada sabbin ministoci a Jamhuriyar Nijar

Sabon shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum Sabon shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum

Shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya nada sabbin ministoci da za su yi aiki a gwamnatinsa.

Sanarwar da Sakataren Gwamnatin kasar ya fitar ranar Laraba ta ce an nada sabbin ministoci 33, shida daga cikinsu mata ne.

Hakan na nufin adadin ministocin ya ragu idan aka kwatanta da ministoci 43 da suka yi aiki a gwamnatin tsohon shugaba Mahaman Issoufou.

An nada ministocin ne a yayin da sabon firaiministan Jamhuriyar ta Nijar Ouhoumoudou Mahamadu ya sha rantsuwar kama aiki.

Ga jerin ministocin:


  • Ministan harkokin waje - Hassoumi Masaoudou


  • Ministan kasa a fadar shugaban kasa - Rhissa Ag Boula


  • Ministan tsaro - Alkassoum Indattou


  • Ministan cikin gida - Alkache Alhada


  • Ministan koyon ayyukan hannu - Kassoum Mahaman Moktar


  • Ministan illimi mai zurfi - PHD Mamoudou Djibo


  • Ministan kiyon lafiya - Dr Illiassou Idi Mainasara


  • Ministan ma'adanai - Mme Ousseini Hadizatou Yacouba


  • Ministan sadarwa ta hanyoyin zamani -Hassane Baraze Moussa


  • Ministan Sufuri - Oumarou Mallam Alma


  • Ministan agajin gaggawa - Lawan Magaji


  • Ministan kiyo kakakin gwamnati - Tijani Abdukadri


  • Ministan gine-gine - Hamadou Adamou Souley


  • Ministan Shari'a - Dr Biubacar Hassan


  • Ministan yada labaru da hulda da sauran hukumomi - Zada Mahamado


  • Ministan Kudi - Ahmat Jidoud


  • Ministan kasuwanci da masana'antu - Gado Sabo Moktar


  • Ministan ayyukan noma - Dr Alambedji Abba Issa


  • Ministan zane-zane da gidaje da tsaftar muhali - Maizoumbou Laoual Amadou


  • li> Ministan fasali - Abdou Rabiou

  • Ministan man fetur da makamashi - Mahamane Sani Mahamadou.


  • Ministan kula da al'adu, yawon bude ido da ayyukan hannu -Mohamed Hamid


  • Ministan inganta kasa da cigaban ci gaban karkara - Maman Ibrahim Mahaman


  • Ministan kula da yaya mata da kari'a kananan yara - Mme Allahoury Aminata Zourkaleini


  • Ministan illimin kananan makarantu - Dr Rabiou Ousman


  • Ministan Albarkatun ruwa - Adamou Mahaman


  • Ministan kwadago - Mme Ataka Zaharatou Aboubacar


  • Ministar muhalli da yaki da kwararar hamada - Mme Garama Saratou Rabiou


  • Ministar kula da ayuka da kariyar al'umma - Dr Ibrahim Boukary


  • Ministan matasa da wasannin motsa jiki - Sekou Doro Adamou


  • Karamin minista a ma'aikatar kudi - Mme Gourouza Magaji Salmou


  • Karamin minista a ma'aikatar cikin gida - Dardaou Zaneidou


  • Karamin minista a ma'aikata harkokin waje - Youssouf Mohamed Almoktar