A ranar Laraba da yamma ne gwamnatin Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta miƙa ƴan matan makarantar sakandaren Jangebe 279 ga iyayensu, bayan da aka gama duba lafiyarsu a gidan gwamnati sakamakon kwanakin da suka shafe a hannun ƴan bindiga.
A daren Juma'ar makon da ya gabata ne ƴan bindigar suka dirar wa makarantar, inda suka sace daliban suka kutsa da su cikin daji.
Bayan mika su a hannun iyayensu, BBC Hausa ta tattauna da biyu daga cikinsu don jin yadda al'amarin ya kasance. Sai dai mun boye sunayen ƴan matan saboda dalilai na tsaro.
- Me ya sa ake satar ɗalibai a Najeriya? ACF ta kalubalanci Matawalle ya fadi sunayen wadanda suka sace daliban Jangebe
Me ya faru lokacin da yan bindigar suka shiga makarantarku?
Amsa daga yarinya ta farko: Lokacin da suka shigo wuraren ƙarfe 1:00 na dare, muna kwakkwance muna barci, can sai muka ji harbe-harbe. Mun zaci malamanmu ne suka zo tashinmu sallar Asuba.To da yake hostel (ɗakin kwana) dinmu ne na farko sai muka ji an banko an shigo. Duk sai muka farka, da muka gansu da bindigogi sai muka fara kuwwa sai suka ce duk wacce ta sake ihu sai sun harbe ta.
Mun shiga cikin tsananin tashin hankali sosai gaskiya. Sai suka ce mu fito suka tara mu duka a waje kamar yadda ake taron makaranta.
Sun taso har da matron dinmu amma sai suka ce ta koma ba sa son tsohuwa. Suka ce mana ina sauran hostels din, mu nuna musu ko su kashe mu. Sai muka nuna musu, sai suka rabu biyu, wasu suka je su taho da sauran daliban mu kuma sauran suka kora mu.
Daga bakin get sai suka fara harbe-harbe, suka bi da mu ta bayan makaranta suka dinga kora mu.
Ke a naki bangaren yaya lamarin ya kasance?
Amsa daga yarinya ta biyu: Kamar yadda 'yar uwata ta bayyana duk haka aka yi. Abin da zan ƙara shi ne kawai a cikin 'yan bindigar har da mata da suka dinga zaginmu ma. Amma tun da aka je sansani aka ajiye mu ba mu sake ganinsu (matan) ba.A wane yanayi kuka tafi ganin cewa dare ne?
Amsa daga yarinya ta farko: Yawancinmu wasu babu takalmi, wasu babu ɗankwali, akwai wata ƙanwata ma rigar bacci ce kawai a jikinta sai a kan hanya ne wasu daga cikinmu da suke da hijabi suka kuma dauko zanin gado shi ne aka ba ta ta lullube jikinta.Wasu kuma da aka kutsa daji sosai sai takalman nasu suka zube.
Yaya tsawon tafiyar ta kasance?
Amsa daga yarinya ta farko: Wallahi tafiya ce mai nisa har ba ta misaltuwa.Suna tsayawa kuna hutawa?
Amsa daga yarinya ta farko:Sai an yi tafiya mai nisa sannan sai masu tausayi daga cikinsu su ce a tsaya ko wajen ƙorama a sha ruwa, da mun sha kuma sai a ci gaba da tafiya a cikin daji.Daji ne mai sarƙaƙiya ga ƙayoyi haka muka yi ta tafiya.
Ba su ɗora ku a kan abin hawa ba?
Amsa daga yarinya ta farko: Ba su zo da babura ba sai da muka kai wajen wani babban dutse da suka ga da yawanmu sun gaza sai suka yi waya suka ce a zo da babura.
Bayan an zo da babura sai aka ce wadanda suka gaji da masu ƙiba su hau, amma sai an zane ki sannan ki hau.
Garuruwa nawa kuka gani a kan hanya?
Amsa daga yarinya ta farko: Tun da muka wuce wasu ƙananan garuruwa na farko kamar Gwaram da Tsibiri da wani da na manta sunansa amma ko su ta bayansu muka ratsa, kuma bayan su ko bukka ba mu sake gani ba.Tafiyar awa nawa kuka yi?
Amsa daga yarinya ta farko: Mun yi tafiya ta kai tsawon ta awa 12. Na kan babura sun riga mu isa, mu kam mun gaji likis. Da muka isa sai muka tarar da wasu 'yan uwansu a wajen wata daba.
Suka ba mu shinkafa fara, sannan suka tara mu duka suka ƙirga mu suka ce mu 200 da wani abu ne.
Sai suka raba mu biyu, suka ce rabi su shiga wani ƙaton kogo kusa da mabiyar ruwa, rabi kuma aka kai su can wani kogon daban. Ba su hada mu waje daya ba.
Idan aka dafa abinci tukunya biyu sai a juye a kan buhu su ce duk mu taru mu ci, wacce ta samu ta yi sa'a wacce ba ta samu ba shi kenan.
Sun ba ku abin shimfida?
Amsa daga yarinya ta farko: A cikin katon kogon nan dai muke kwanciya sai suka ba da katon buhu suka ce mu shimfida, ko bai ishe mu ba mu muka sani.Daga baya da suka ga jirgi na shawagi ta wajen sai suka sauya mana waje suka kai mu filin Allah tarwal ga tsananin sanyi haka muka ci gaba da kwana.
Wa yake dafa abinci?
Amsa daga yarinya ta farko:A cikinmu suka zabi wadanda ke dafawa. Sai mutum biyu cikinsu su tasa wasu ɗaliban a gaba su je gulbi su ciko jarkoki da ruwa su kawo.A wannan ruwan ne su 'yan bindigar suke wanka su yi bukatunsu su kuma sha, amma mu iyakarmu mu yi girki da shi mu dan sha.
Sun yi kokarin cin zarafinku?
Amsa daga yarinya ta biyu: Sun yi ta zaginmu dai sosai amma ba su yi kokarin taba mana mutunci ba. Sukan ɗuɗɗura mana zagi cewa da maza ne mu da sun doke mu. Amma dai babu cin zarfi baya ga zagi.A ranar farko ma da muka je sai da shugabansu ya ja mana kunne cewa duk wacce wani namiji ya taba ta ba ta yi ihu ko ta fada ba to sai ya hada ita da mutumin ya kashe su.
Ta yaya kuke biyan bukatunku?
Amsa daga yarinya ta biyu:Idan mutum na jin fitsari sai su ce ka dan zagaya baya kadan daga inda muke ka yi. Idan kuma kashi kake ji sai a ce ka je can gaba sosai ka yi. Amma fa ba ma yin tsarki haka muke zama.Sukan ce wata ta raka wata ma, sai su ce ai mu mata ne ba za mu iya gudu ba. Amma dai ni al'ada ba ta zo min ba, sai dai na tabbata ko da al'ada ta zo wa wata ma to sai dai ta zauna haka.
Kuna wanka?
Amsa daga yarinya ta biyu: Tun da muka je ba ma wanka ba ma wanke jiki. Kuma ba ma sallah tun da muka je. Sai dai idan sun kora mu shan ruwa wajen ƙorama tamkar dabbobi, to a can muke dan wanke fuska.Suna waya a gabanku?
Amsa daga yarinya ta biyu: Eh amma da Fillanci suke magana. Sai idan sun gama sai su zage mu su ce idan har gwamnati ba ta kawo kudin fansa ba to kashe mu za su yi.Amma wasu daga cikinsu sai su ce mu kwantar da hankalinmu ba za su kashe mu ba.
Ranar tafiya
Amsa daga yarinya ta farko: Ba su gaya mana ba sai bayan da muka ci abincin dare sai suka ce mu kama tafiya. Ba su ce mana komai ba sai da wasunmu suka gaji suka koka sai suka ce don ubanmu mu yi shiru ai gidan ubanmu za mu tafi.To sai muka fara murna da shewa, amma suka hana mu.
Wasu da dama daga cikinmu sun yi rashin lafiya a can ko tashi ba sa iya yi. Da aka dawo gida sai da aka kwantar da su a asibiti.
Za ku koma makaranta?
Yaran biyu duk sun amsa wannan tambayar da cewa: Eh idan dai tsaro ya inganta za mu koma, don gaskiya muna son karatu.Wannan abin ba zai karya mini gwiwa ba. Amma gaskiya muna so gwamnati ta zuba jami'an tsaro masu yawa na dindindin a makarantar don idan muka koma mu samu kwanciyar hankali.