BBC Hausa of Wednesday, 17 March 2021

Source: BBC

Musulmai da Kirista na ce-ce-ku-ce kan batun saka hijabi a makarantun Kwara

A ranar Laraba ne fada ya ɓarke tsakanin Musulmai da Kiristoci a Ilorin A ranar Laraba ne fada ya ɓarke tsakanin Musulmai da Kiristoci a Ilorin

Ƴan Najeriya da dama sun yi ta bayyana albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta da muhawara kan rikicin da ya ɓarke tsakanin Musulmai da Kiristoci kan batun saka hijabi a wasu makarantun jihar Kwara.

A ranar Laraba ne fada ya ɓarke tsakanin Musulmai da Kiristoci a Makarantar Sakandare Baptist da ke birnin Ilori na jihar Kwara, a yankin tsakiyar Najeriya kan batun barin ƴan makarantar su sanya hijabi.

An ƙaddamar da maudu'i mai taken #Kwara da #Hijab a shafin sada zumunta na Twitter inda aka yi amfani da su fiye da sau sama da 12,000 da kuma sau sama da 6,000.

Me ake cewa a Tuwita?

Ra'ayoyi sun sha bamban a shafin Tuwita, yayin da wasu ke ganin laifin hukumomin makarantun, wasu kuwa laifin iyayen yaran suke gani.

Masu ganin laifin iyayen yaran na cewa idan har tsarin makarantun bai musu ba to kamata ya yi su cire su, musamman tun da sun san cewa makarantun na mabiya addinin kirista ne.



Aisha Yesufu ta ce: "Me ya sa wani zai dage kan batun yadda ya kamata makarantar kuɗi ta yi tsarin kayan da ɗalibanta za su sa.

"Idan makarantar gwamnati ce to wannan wani abu ne daban. Idan har ba sa son ɗalibansu su sanya hijabi, ku a matsayinku na iyaye kuma kuna son ƴaƴanku su saka hijabi, sai kawai kar ku kai su can.




Shi kuwa wani tsohon sanata daga jihar Kaduna Shehu Sani cewa ya yi: "Ƴan gani kashenin addinin a Ilori da suke faɗa kan hijabi ya kamata su adana kuzarinsu da mayar da hankali wajen kare jiharsu daga ƴan bindiga da a hankali suke kutsawa daga jihar Neja.