BBC Hausa of Wednesday, 14 April 2021

Source: BBC

Musulmin Afirka za su yi azumin Ramadana na biyu cikin annoba

Kasar Masar ta hana yin sallar jam'i a masallatai Kasar Masar ta hana yin sallar jam'i a masallatai

Musulmi a duk fadin Afirka za su fara azumin watan Ramadan mai alfarma wanda zai fara daga ranar Talata.

A shekara ta biyu, dokokin takaita taruwar jama'a na ci gaba da aiki cikin wasu ƙasashe a cikin watan azumin ramadana.

Kasar Masar ta hana yin sallar jam'i a masallatai.

Firai Ministan Tunisia Hichem Mechichi ya mara baya a ranar Lahadi kan shawarar tsawaita awanni na dokar hana fitar dare, bayan damuwar da aka nuna ga rayuwar mutane.

Mista Mechichi, wanda ya dade yana rashin jituwa da Shugaba Kaïs Saïed, a ranar 7 ga Afrilu ya ba da sanarwar cewa dokar hana fita da aka sanya domin dakile yaduwar annobar korona za ta fara ne daga karfe 7 na yamma agogon kasar (18:00 GMT), maimakon 10 na dare gabanin Ramadan.

Bayan kwana biyu, Mista Saïed ya yi kira ga Firai Minista da ya sake nazarin shawarar, don kaucewa asarar dubban ayyuka a cikin watan mai alfarma wanda Musulmi ke azumi a ciki har faduwar rana.

A bara , shugabannin Afirka sun aike da sakonnin Ramadan na musamman na fatan alheri ga Musulmin da ke nahiyar yayin da aka zartar da dokokin dakile bazuwar cutar korona masu tsauri.