BBC Hausa of Friday, 7 May 2021

Source: BBC

Mutuwar Sarkin Zulu Zwelithini: 'Yan gidan sarauta da masu adawa suna fafatawa domin hawa karagar mulki

Sarautar Zulu a Afirka ta Kudu ta faɗa cikin rikici sanadin mutuwar Sarki Goodwill Zwelithini Sarautar Zulu a Afirka ta Kudu ta faɗa cikin rikici sanadin mutuwar Sarki Goodwill Zwelithini

Sarautar Zulu a Afirka ta Kudu ta faɗa cikin rikici sanadin mutuwar Sarki Goodwill Zwelithini sannan ƴan makwanni tsakani shugabar riƙon ƙwaryar masarautar ta mutu.

Hakan ya haifar da sabuwar gwagwarmayar neman sarauta inda masu neman mulkin ke fafatawa a kotu da yi wa juna shaguɓe a bainar jama'a da kuma yaɗa jita-jita kan abokan hamayya.

Wakiliyar BBC Pumza Fihlani da ke Johannesburg ta duba wasu daga cikin masu taka rawa da abin da ke faruwa a masarautar:

Uban Ƙasa: Sarki Goodwill Zwelithini

An haife shi ranar 14 ga watan Yulin 1948 kuma shi ne sarki na takwas a masarautar Zulu. Kafin ya hau kan kujerar sarautar bayan rasuwar mahaifinsa a 1971, sai da ya shafe shekara uku yana ɓoye saboda barazanar kashe shi da ake yi.

Isilo Samabandla Onke, da ke nufin "Sarkin Sarakunan Zulu," kamar yadda ake kiransa ya fito ne daga zuriyar Sarki Cetshwayo, shugaban Zulu a yaƙin da aka yi da sojojin Birtaniya a 1879.

Ga mutane da dama, Sarki Zwelithini, mai ƴaƴa 28 daga mata shida, yana girmama al'ada matuƙa. Wata bajinta da aka yi a zamaninsa ita ce farfaɗo da bikin gargajiya na 'Reed' a 1991.

Bikin, wanda ɗaruruwan matan Zulu da ba su da aure suke halarta, ana yinsa ne domin taya murnar budurcin ƴan mata amma Sarki Zwelithini ya ce ana yin bikin domin ƙara wayar wa mutane kai kan cutar HIV/Aids a KwaZulu-Natal - wani Lardi da ya zama da mutanen da ke da cutar suka fi yawa a ƙasar.

Sarki Zwelithini ya mutu ranar 12 ga watan Maris a wani asibiti inda ya yi jinya kan rashin lafiyar da ke da nasaba da ciwon suga. Shi ne Sarkin Zulu da ya fi daɗewa kan mulki- ya kwashe kusan shekara 50 kan karaga.

Bayan binne shi, an karanta wasiyyar da ya bari a wani taro na sirri da aka yi a masarautar. Wasiyyar da ya bari na cikin abubuwan da ake ce-ce-ku-ce a kai a tsakanin iyalan masarautar inda wasu daga ciki ke iƙirarin kawai a manta da ita.

Mai nadin sarauta: Sarauniya Mantfombi Dlamini-Zulu

A cewar wasiyyar, Sarkin ya zabi Sarauniya Mantfombi Dlamini-Zulu a matsayin wadda za ta zama shugabar rikon kwarya ta masarautar ƙasar mai al'umma miliyan 11.

Sarauniya Dlamini-Zulu ce ya kamata ta ci gaba da mulki har zuwa ƙarshen wata uku na jimamin mutuwar Sarkin sannan an sa ran ita ce za ta fadi wanda zai gaji Sarkin sai dai ta mutu kafin hakan ta faru.

Ƴar uwa ce ga Sarkin Eswatini wato Mswati III sannan ta auri Sarkin Zulu a 1977.

Ta fito daga gidan sarauta kuma tana da ƴaƴansu takwas da marigayin.

Sai dai saɓanin sauran matan Sarki, an biya sadakinta da shanu 300. Masana tarihi sun ce hakan ya ƙara tabbatar da babban matsayinta a gidan sarautar.

An naɗa ta a matsayin shugabar riƙon ƙwarya bayan raɗe-raɗin cewa babban ɗanta Yarima Misizulu mai shekara 46 da ya yi karatu a Amurka shi ne zai gaji sarautar Zulu sai dai masarautar ba ta tabbatar da hakan ba.

Sarauniyar ta mutu tana da shekara 65 sakamakon rashin lafiyar da ba a bayyana ta ba wata daya bayan ta zama shugabar riƙon ƙwarya kuma aka binne ta ranar Alhamis. Mutuwar Sarauniyar ranar 29 ga watan Aprilu ta bar tambayoyi a zukatan mutane da dama tare da janyo jita-jita game da kitsa kashe ta.

A shekarun baya-bayan nan, ta shafe lokaci mai tsawo a Eswatini domin kula da lafiyarta.

A wani lokacin kuma, da Sarki ya yi bayani kan rashin kasancewar Sarauniyar a Zulu, ya ce an zuba mata guba ne.

"Sarkin ya yi magana gaban ɗaruruwan mutane a Disambar 2017 lokacin da aka taru domin bikin cikarsa shekara 46 kan karagar mulki. A gaban mutanen, Sarkin ya ce: "An zuba wa Mnemtanenkosi guba. Shi ya sa ba ta nan tare da mu," kamar yadda Firaministan Zulu Chief Mangosuthu Buthelezi ya faɗa cikin wata sanarwa a farkon makon nan.

Baa fitar da wasu ƙarin bayanai ba game da iƙirarin ba ta gubar daga 2017 amma an gano cewa tana yawan zuwa asibiti tun lokacin.

Har yanzu dai ba a ba da bayani ba kan abin da ya haddasa mutuwarta. Chief Buthelezi ya ce an yi bincike kan gawarta sannan ana dakon samun sakamakon binciken cikin makwanni.

"Lokacin da na sanar da mutuwar Sarauniya, na yi magana da harshen isiZulu inda na yi bayani cewa likitoci ba sa son yi mata aiki saboda gubar da aka gani a hantarta. Hakan ya sa aka ba ta wasu magunguna da aka yi tunanin za su rage ciwon." kamar yadda aka rawaito ya faɗa dai-dai lokacin da ake ta raɗe-radin cewa an sake zuba mata guba.

Sarauniya Sibongile Dlamini

Ita ce matar Sarki Zwelithini ta farko da ta nemi kotu ta ba ta rabin dukiyar mijinta da ya mutu da ya hada da wasu dukiyoyinsa da filaye a sassan KwaZulu-Natal mallakin Sarkin.

Babu bayanai kan yawan dukiyar da Sarkin ya bari. Gwamnatin KwaZulu-Natal tana biyan masarautar dalar Amurka miliyan 5 duk shekara domin tafiyar da gidan.

Sarauniya Dlamini tana neman kotu ta kashe auren da ke tsakanin Sarkin da sauran matan biyar domin hana su samun damar mallakar kadarorin don ta zama ita kadai ce matarsa ta aure sannan ta hana wani da bai fito daga dakinta ba damar hawa kan karagar mulkin.

Ta ce ita ce take riƙe da muƙamin "Uwargida ran gida," ko Udlunkulu a Zulusaboda ita ce matar Sarkin ta farko da ta aure shi ƙarƙashin dokar ƙasa wadda ba ta yadda da auren mace fiye da daya ba.

A takardar kotun, Sarauniya Dlamini ta kuma bayyana cewa an tilasta mata auren Sarki Zwelithini ƙarƙashin tsohuwar al'adar nan ta ukuthwala tana da shekara 20.

"An kai ni gidan marigayi Isilo ta al'adar ukuthwala domin auren marigayin domin ya samu hawa kan kujerar mulki a matsayin Sarkin Zulu," a cewarta.

Ta yi iƙirarin cewa masarautar tata ce, ita da mijinta marigayi kuma duk wani yunƙuri na soke hakan bai dace da doka ba".

A wata takardar kotun kuma, biyu daga cikin ƴaƴan Sarauniya Dlamini na ƙalubalantar sahihancin wasiyyar da mahaifinsu ya bari inda suka bayyana cewa suna da dalilinsu da zai sa su yadda cewa tsara wasiyyar aka yi. Sun goyi bayan Sarauniya Dlamini kan batun mallakar dukiyar mahaifinsu.

Yariman da ya mutu: Lethukuthula

Tsawon shekaru akwai raɗe-radin cewa Sarkin zai zaɓi babban ɗansa Yarima Lethukuthula a matsayin magajinsa. Yariman da ne ga matar Sarki ta farko.

Amma yariman ya mutu cikin watan Nuwamba a wani yanayi da ba a iya tantance sa ba. Wasu daga masarautar na ganin mutuwarsa na da nasaba da ƙoƙarin da ake na hana shi gadar mahaifinsa sai dai babu wasu bayanai da suka tabbatar da hakan.

An kama mutanen da ake zargi biyar - huɗu mata da shekarunsu yake tsakanin ƴan shekara 27 da 42 da kuma wani mutum mai shekara 32 a Pretoria bisa kisan Yariman mai shekara 50.

Ana ci gaba da binciken da aka yi game da mutuwarsa sannan kawo yanzu ba a bai wa mutanen damar roƙo ba.

Rahotannin farko sun yi zargin cewa wadanda ake zargin sun zuba wa Yariman da abokiyar kasuwancinsa guba da yi musu sata.

An ga gawar Yariman daga baya sannan abokiyar kasuwancinsa kwance a wani ɗaki.

Mia magana da yawun masarautar ya bayyana cewa ba a iya samarwa dukkanin ƴaƴan sarkin tsaro ba saboda abu ne da zai kasance da tsada.

Yan tawayen Masarauta: Yarima Mbonisi da Gimbiya Thembi

Ƴan kwanaki bayan mutuwar Sarki, an zargi ƴan uwansa Yarima Mbonisi da Gimbiya Thembi da gudanar da wani taron sirri. Da alamu ba sa goyon bayan nada Sarauniya Dlamini-Zuli a matsayin shugabar riƙon ƙwarya.

Labarin tarukan ya sa wasu ba su ji dadi ba musamman wadanda ke tunanin hakan zai janyo rarrabuwar kai a masarautar.

Amma ƴan uwan Sarkin sun musanta zargin inda suka ce suna tattaunawa ne kan yadda za su bai wa Shugabar riƙon ƙwaryar goyon baya kuma suna da niyyar kai rahoto ga masarautar.

Sun kuma nisanta kansu daga hannu a mutuwar Sarauniyar.

"Mutane na tunanin mu masu kisa ne," Gimbiya Thembi ke faɗa wa kafafen yaɗa labarai ranar Lahadi a wani taron manema labarai da aka yi yayin da ake ci gaba da tsokaci kan wanda zai gaji sarautar.

Ta ƙara da cewa ba wai suna "kitsa yadda za su tsige kowa ba".

Kakaki: Chief Mangosuthu Buthelezi

Tun mutuwar Sarki Zwelithini, Chief Buthelezi yake ta magana kan abin da ke faruwa a masarautar.

Ana yi masa kallon Firaministan gargajiya sannan ya taka rawa wajen sanar da mutuwar Sarkin da shugabar rikon ƙwarya da kuma sanar da jama'a tsare-tsaren jana'iza.

Amma matsayinsa ya sa wasu ƴan sarautar na jin haushinsa har suke zarginsa da murƙushe masu hamayya da nuna isa sannan sun yi fatali da iƙirarin cewa shi ne Firaministan gargajiya na Sarki Zwelithini ko babban mashawarcinsa.

"Wa'adinsa muƙaminsa na Firaministan gargajiya ya ƙare da jimawa. Dalilin da ya sa har yanzu yake kan muƙamin shi ne muna girmama shi," kamar yadda aka rawaito Gimbiya Thembi na faɗi.

Sai dai Chief Buthelezi ya ce Gimbiyar ba ƴar baffansa Sarki Cyprian ba ce da aka haifa ta hanyar aure kuma ya bayyana Yraima Mbonisi a matsayin dan aiken Sarki.

Babu bayanai game da yadda za a warware rikicin shugabancin da kuma lokacin da za a sake zaɓar sabon sarki. Amma ana ta matsa lamba kan iyalan masarautar su tabbatar an yi nadin cikin lumana da tsari. MasarautaR ta ƙunshi abubuwan al'ada da dama da ƴan Zulu ke girmamawa.