BBC Hausa of Tuesday, 18 May 2021

Source: BBC

Nasir El-rufa'i na neman shugaban kungiyar kwadago ruwa a jallo

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai

Gwamnan Kaduna Nasir Ahmed El-Rufa'i ya ce yana neman Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, Ayuba Wabba da wasu mutane ruwa a jallo.

Gwamnan ya ce ana nemansu ne bisa laifin yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa da lalata kayan gwamnati ƙarƙashin dokar laifuka ta Miscellaneous Offences Act.

El-Rufa'i ya ce duk wanda ya san inda yake ɓuya ya sanar da Ma'aikatar Shari'a ta jihar inda za a ba shi kyauta mai tsoka.

A ranar Talata ne aka shiga rana ta biyu na yajin aikin gargadi da kuma zanga-zangar da 'yan kungiyoyin kwadago suka fara a jihar ta Kaduna.

Ita dai Kungiyar Kwadago ta NLC ta lashi takobin ci gaba da zanga-zanga da kuma yajin aiki ne sakamakon abin da ta ce kin amincewar gwamnatin jihar na soke matakin sallamar dubban ma'aikata.

To sai dai a nata bangaren, gwamnatin jihar ta zargin kungiyar da yi mata zagon kasa.

Yajin aikin da kuma zanga-zangar da kungiyoyin kwadago ke yi a jihar sun janyo tsaiko a akasarin ma'aikatu, da asibitoci da ma makarantun gwamnati a fadin jihar inda galibin ma'aikata suka shiga cikin yajin aikin.

Duk da yake a jiya Litinin wato rana ta farko ta yajin aikin, jama'a sun ci gaba da zirga-zirga kamar yadda suka saba, sai dai kusan akasarin gidajen sayar da man fetur sun kasance a rufe.

Lamarin ya haddasa karancin man fetur din yayin da kuma aka datse hanyoyin samar da wutar lantarki a fadin jihar - matakin da ya jefa dubban jama'a zama cikin duhu.

A bangare guda kuma, ko da yake kasuwanni da dama sun buɗe, sai dai harkokin kasuwanci ba sa tafiya kamar yadda aka saba gani, abin da ya wasu 'yan kasuwa suka gwammace su yi zamansu a gida.

Kungiyar Kwagado ta NLC dai ta ce a yau Talata ma za ta ci gaba da gudanar da gangami kamar yadda ta fara a jiya don nuna wa duniya gallaza wa ma'aikata da take zargin gwamnatin jihar ƙarƙashin Nasir El_Rufai da aikatawa ta hanyar sallamar dubban ma'aikata ba tare da biyan haƙƙoƙinsu ba.

Sai dai a wata sanarwa da ta fitar da yammacin jiya, gwamnatin Kaduna ta yi Allah-wadai da zanga-zangar da kuma yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadagon ke yi.

Sanarwar da mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin watsa labarai Mr Muyiwa Adekeye ya sanya wa hannu - ta ce irin munanan kalamai da 'yan ƙwadagon ke danganta su da gwamnatin jihar ba za su canza komai ba.

Sanarwar ta kuma yi zargin cewa duk da irin yunƙurin da 'yan ƙungiyar NLC suka yi na neman hana wasu ma'aikata shiga sakatariyar gwamnatin jihar don gudanar da ayyukansu, haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.

Gwamnatin ta kuma zargi ƙungiyar da rufe asibitocin gwamnati da dama a faɗin jihar tare da korar majinyata da suka je don neman magani - ba ya ga uwa uba datse hanyoyin samar da wutar lantarki, abin da ta ce alama ce ta nuna tsabar rashin imani.

Kuma a cewar gwamnatin, tana nan tana tattara bayanai kan irin waɗannan ayyuka da suka saɓa wa ka'ida.

Ita dai gwamnatin Kaduna a sanarwar da ta fitar ta buƙaci al'ummomin jihar su ƙara haƙuri kan mawuyacin halin da suka shiga, inda ta ce zanga-zangar ta 'yan ƙwadago wata manuniya ce ƙarara kan yunƙurin yi mata zagon ƙasa.

A ɓangare guda kuma rundunar 'yan sandan ƙasar ta ce ta tura ƙarin jami'an tsaro da kayan aiki zuwa babban titin Kaduna zuwa Abuja, wanda ya yi ƙaurin suna kan satar mutane don neman kuɗin fansa bisa tsammanin samun ƙaruwar ababen hawa saboda rufe filin jirgin sama da tashar jirgin ƙasa a Kaduna, jihar da ke haɗa mafi yawan yankin arewacin ƙasar da kudanci.