BBC Hausa of Thursday, 29 April 2021

Source: BBC

Nau'in gahawar da ke jure wa tasirin sauyin yanayi

Coffea stenophylla ce gahawar Coffea stenophylla ce gahawar "da aka manta" cewa yana tsirowa a cikin yanayi mai dumi

Masana kimiyya sun ce nau'in gahawar "da aka manta" cewa yana tsirowa a cikin yanayi mai dumi ka ya taimaka wa makomar shan gahawa a yayin da ake fama da matsalar sauyin yanayi.

Sun yi hasashen cewa ba da jimawa ba kurbar Coffea stenophylla, wata gahawar da ke tsirowa da kanta da kuma dandanonta ke kama da na nagartacciyar gahawar Arabica, amma tana tsirowa ne a yanayi mai dumi.

Yayin da yanayin zafi ya karu, gahawa mai kyau za ta kara kasancewa mai wuyar tsirowa.

Bincike ya nuna cewa nan da shekara ta 2050, kusan rabin filin da ake amfani da shi wajen shuka nagartacciyar gahawa zai kasance marar amfani.

Samun gahawar da ke tsirowa da kanta da kuma ke da dadin dandano kana mai jure wa lokacin fari "wata babbar kyauta ce," in ji Dakta Aaron Davis, shugaban lambun binciken shuke-shuke kan gahawa ta Royal Botanic Gardens, Kew.

Ya shaida wa BBC cewa "Kasancewar wanda ya taba dandana irin wannan nau'in gahawar da dama ba su da wani kyau, ba su da dandano irin na Arabica, don haka tunaninmu a kan nagartarsa ba shi da yawa.

"Kuma hankalinmu ya dauke gabaki daya aka tunanin cewa wannan nau'in gahawa na da dadin dandano. Tana da wadannan darajoji da ke da alaka da jure wa sauyin yanayi: Za ta tsiro ta kuma girma a karkashin yanayi mai dumama fiye da nau'in gahawa na Arabica."

Coffea stenophylla nau'in gahawa ce da ke tsirowa da kanta a yankin Afirka taYamma, a baya an dauka cewa wannan nau'i ya riga ya bace daga kasar Ivory Coast.

An sake gano shukar na fitowa a kasar Saliyo, inda tarihi ya nuna cewa nan ne ake nomanta a matsayin shukar gahawa a karnin da ya gabata.

Ana gasa ta samfurin kwayoyin gahawa daga kasashen Saliyo da Ivory Coast a kuma sarrafa shi zuwa gahawa, wanda kuma akan tara mutane masu dandanawa su yi alkalanci .

Kusan kashi 80 bisa dari na alkalan sun gaza gano bambanci tsakanin nau'in gahawa na Stenophylla da na Arabica a wasu gwaje-gwajen da aka yi idanu rufe, masu bincike sun bayar da rahoton a mujallar ''Nature Plants''.

Sun kuma tattara bayanan sauyin yanayi kan shukar, da suka nuna cewa za ta iya jure wa yanayin zafin da ya kai ma'aunin 6C fiye da nau'in Arabica.

Za a shuka irin a cikin wannan shekarar don fara duba yanayin yadda irin wannan gahawa za ta kare martabar nagartacciyar gahawa nan gaba.

Dakta Davis na fatan wata rana za a sake noma nau'in gahawar na Stenophylla a kasar Saliyo mai yawan gaske.

"Ba wai za a samu shagunan shan gahawa ba ne a cikin 'yan shekaru, amma ina ga a cikin shekaru biyar zuwa bakwai za mu ga tana shiga kasuwannin da manyan kantunan sayar da gahawa, a matsayin gahawa mai daraja, bayan nan ne kuma za ta kasance a ko ina," in ji shi.

Mece ce gahawar Arabica?

Kwayoyin gahawar Arabica na da mafi dadin dandano. Ana nomawa a cikin tsaunuka kuma tana samar da kashi 60 bisa dari na irin gahawar da ake nomawa a duniya.

Arabica tana da karancin juriya kan sauyin yanayi; manoma sun fara fuskantar mummunan tasirin karuwar yanayin zafin da kuma karanci ko mamakon ruwan sama.

Sauran abubuwan da kan haifar dabarazana ga noman gahawa sun hada da yawan sauyin farashi, kwari da cututtuka da kuma yanayi mai tsanani.

An gudanar da binciken ne da hadin gwiwar cibiyar bincike ta kasar Faransa Cirad da kuma Jami'ar Greenwich.

Ina ake samun nau'in gahawar stenophylla?

Akasarin nau'ukan gahawar kan tsiro ne a kungurmin dazuka na Afirka da kuma tsibirin Madagascar. Baya ga Afirka, an samun wannan nau'i a sauran yankunan kasashe masu zafi da suka hada da India, da Sri Lanka, da kuma Australia.

Wane irin nau'in gahawa ne muke sha?

Nau'ukan bishiyoyin gahawa fiye da dari ke fe tsirowa a cikin dazuka, amma kadan ne daga ciki ake iya sarrafawa domin sha.

Manyan nau'ukan gahawa biyu ne suka mamaye masana'antar sarrafa gahawar ta duniya - Arabica (Coffea arabica) da kuma Robusta (Coffeea canephora).

Ana noma nau'i na uku - Liberica (Coffea liberica) a fadin duniya, amma ba a cika amfani da shi wajen sarrafa gahawar domin sha ba.