Dan kwallon Brazil, Neymar ya ce yanzu batun makomarsa a Paris St Germain kan tsawaita zamansa a Faransa ba wani babban lamari ba ne da ke jan hankali.
A shekarar 2017, Paris St Germain ta dauki Neymar daga Barcelona kan dalar Amurka miliyan 265.60 a matakin mafi tsada a fanni tamaula a duniya.
Dan kwallon tawagar Brazil ya ci Ligue 1 uku da French Cup biyu tun komawarsa Faransa da taka leda, kuma ya taka rawar gani da PSG ta kai wasan karshe a Champions League a bara.
Neymar wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen Yunin badi, ya kira kungiyar ta Faransa da cewa ''gida ce a wuri na''.
Neymar ya ci wa PSG kwallo shida a gasar Zakarun Turai da ake buga wa, shi kuwa Kylian Mbappe ya zura takwas a raga a ba.
Ranar Talata PSG ta kai wasan daf da karshe a Champions League na bana, duk da doke ta 1-0 da Bayern Munich ta yi a Faransa.
Ranar Laraba kungiyar ta Faransa ta je ta ci Bayern Munich 3-2 a wasan zagayen farko a quarter final a Jamus.