BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: BBC

Rahoto: Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a wannan makon

Shafin BBC ke gabatar da muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya Shafin BBC ke gabatar da muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya

Wannan maƙalar na ƙunshe da muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a wannan makon.

Daga ciki akwai; EFCC za ta binciki duk wani ɗan Najeriya da ke rayuwar da ta fi ƙarfinsa; Wasu jiga-jigan kabilar Yarabawa sun nesanta kansu daga ballewa daga Najeriya; Hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum 19 a Kaduna.

Yadda 'wata uwargida ta kashe' amarya mai kwana 54 a jihar Neja

Rundunar 'yan sandan jihar Neja a Najeriya ta tabbatar da kisan da wata mata ta yi wa kishiyarta mai suna Fatima wacce ba ta cika watanni biyu da auren ba ta hanyar duka da ƙona ta.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Mohammed Adamu ya shaida wa BBC cewa, sun samu labarin ne bayan da mijin matar mai suna Aliyu Abdullahi ya kai musu rahoto kan faruwar lamarin inda ya ce ya shiga gida ya taras an kashe amaryarsa.

Kuma in ji shi, binciken da suka gudanar ya nuna cewa an yi ta dukanta da taɓarya ko wani abu mai ƙarfi ne kafin a ƙona ta "don nuna cewa ta mutu ne a sakamakon gobara."

Tuni dai aka yi jana'izar marigayiyar a gidan iyayenta da ke Katsina.

Ya ce "Akwai alamun cewa ita uwargidan da wata ƙawarta da ta taimaka mata sun yi mata dukan gaske da taɓarya ko kuma wani abu mai ƙarfi kafin su ƙona ta, saboda duk da cewa ta ƙone akwai alamun duka a jikin gawar, mun kai gawar asibiti inda aka duba ta kafin mu miƙa wa danginta domin yi mata jana'iza."

Kwamishinan 'yan sandan ya kuma kara da cewa yanzu haka uwaridan wato wacce ake zargi da aikata kisan na hannunsu tare da sauran mutum uku da suka taimaka mata.

Kuna iya karanta cikakken labarin a nan: Yadda 'wata uwargida ta kashe' amarya mai kwana 54 a jihar Neja

EFCC za ta binciki duk wani ɗan Najeriya da ke rayuwar da ta fi ƙarfinsa - Gwamnati

Mataimakiya ga shugaban Najeriya kan kafofin sada zumunta, Laurette Onochie, ta ce hukumomin da ke yaƙar rashawa wato EFCC da ICPC za su binciki ƴan Najeriya da ke rayuwar da ta fi ƙarfinsu musamman a shafukan sada zumunta.

Ms Onochie ta shaida hakan ne a shafinta na Twitter ranar Litinin, tana mai cewa za a gayyaci irin wadan nan mutane domin bincike kan yadda suka mallaki kadarorin da arzikin da suke nunawa.

Onochie ta ce, "bincikar yadda mutum ya ke rayuwarsa za ta kasance wajibi a Najeriya bisa sharuɗa na doka".

Wannan na zuwa ne bayan a makon da ya gabata, shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya fitar da sanarwa cewa wajibi ne duk wani ma'aikacin banki ya bayyana kadarorin da ya mallaka.

'Yan sanda a Kano sun kama mutumin da ake zargi da sama wa 'yan bindigar Zamfara babura

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta cafke wani mutum da take zargin yana sama wa 'yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar Zamfara babura.

Rundunar ta kama mutumin ne a jihar Kano, inda bayanai suka ce yana sayen babura domin tafiya da su jihar ta Zamfara, ya kuma sayar wa yan bindigar a kan farashi mai yawan gaske.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce yayin binciken da suka gudanar mutumin ya shaida musu cewa ya sayarwa da 'yan bindigar babura kusan 100, a kan sama da Naira dubu dari shida duk ɗaya.

Ya ƙara da cewa mutumin kan baro Zamfara zuwa Kano ya sayi baburan sannan ya sake komawa can domin sayarwa yan bindigar, amma sai a yanzu aka kama shi, bayan samun bayanai daga wajen waɗanda yake sayan baburan a wajensu a jihar ta Kano.

"Babur yake sayarwa kirar Honda ACE 125, wanda ake kiransa da Boko Haram a can jihar Zamfara, wanda tuni gwamnatin jihar ta hana amfani da shi, in suka zo jihar Kano sai su saya su canja musu kwali, a haka suke shigar da shi daji, inda a can ake hada shi, sannan su yi amfani da shi wajen kai wa mutane hare-hare."

Hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum 19 a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce mutum 19 ne suka mutu sakamakon hatsarin motar da ya rutsa da su a yankin Kateri da ke kan titin Kaduna zuwa Abuja ranar Lahadi da yamma.

Sanarwar da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya wallafa a shafin Tuwita na ma'aikatarsa, ta ce lamarin ya faru ne sakamakon fashewar da tayar wata tirela da ke mugun gudu ta yi, abin da ya sa ta kubce wa direbanta ta shiga daji.

"Lamarin ya shafi mutum 53; 16 daga cikinsu sun mutu nan take, yayin da mutum uku suka mutu daga bisani. Mutumu 34 sun jikkata," a cewar sanarwar.

Ta kara da cewa mutanen da suka jikkata suna can a asibiti inda ake kula da lafiyarsu.

Wasu jiga-jigan kabilar Yarabawa sun nesanta kansu daga ballewa daga Najeriya

Wasu jiga-jigan Yarabawa sun nesanta kansu daga matakin da mai ikirarin fafutukar nema wa kabilarsu 'yanci ya dauka na cire Yarabawa daga Najeriya domin kafa kasarsu.

A kwanakin baya ne Sunday Igboho ya ce kabilar Yarabawa za ta balle daga Najeriya saboda rashin adalcin da ake yi mata.

A cewarsa, shi da wasu masu ra'ayi irin nasa sun dauki matakin ballewa daga Najeriya ne sakamakon kashe-kashen da makiyaya suke yi wa Yarabawa a jihohin kudu maso yammacin kasar.

Ya yi kira ga dukkan Yarabawa su amince da matakan da shugaban kungiyar kafa kasar Yarabawa ta Nigerian Indigenous National Alliance for Self-determination, Farfesa Banji Akintoye yake dauka na tabbatar da kasar Yarabawa mai cin gashin kanta.

A baya bayan nan Sunday Igboho ya jagoranci wasu masu ikirarin kare hakkin Yarabawa inda suka rika korar Fulani makiyaya daga jihohin kudu maso yammacin Najeriya.

Ya zargi Fulanin da ke yankin da kitsa garkuwa da mutane da kashe-kashe da kuma wasu laifuka da ke faruwa a yankin.

Za a iya janye tallafin man fetur a kowanne lokaci - NNPC

Shugaban kamfanin mai na ƙasa, NNPC, Mele Kyari ya ce gwamnatin na biyan naira biliyan 120 a kowanne wata a matsayin tallafin man fetur.

Kyari ya fadi hakan ne a taro na musamman da ministoci ke yi wa manema labarai bayani karo na biyar da aka gudanar a fadar gwamnatin Najeriya a Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kyari ya ce, a maimakon ƴan ƙasar su dinga sayen mai kan yadda farashin kuɗaɗen shigo da adana shi suke na naira 234 kan kowace lita guda, gwamnati na sayar da man a kan naira 162, don haka ita ke ɗaukan nauyin cikon kuɗin.

Sai dai ya ƙara da cewa, NNPC ba zai iya ci gaba da asarar waɗan nan kuɗaɗe ba, don haka ƴan Najeriya nan bada jimawa ba za su koma sayen man yada aka samo shi.

Ya kuma shaida cewa dole ne a bar kasuwa ta ƙayyade yadda farashin mai zai kasance a ƙasar.

'Yar Kano ta lashe musabakar Ƙur'ani ta mata, ɗan Zamfara ya lashe ta maza

Ranar Asabar ce aka kammala musabakar Al-kur'ani mai girma ta kasa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

An fara musabakar ne kwanaki takwas baya, inda a yau kwana na tara aka kammala ta.

Muhammad Auwal Gusau, shi ne gwarzon musabakar ta bana bangaren maza, kuma ya fito ne daga jihar Zamfara.

Ya kara da masu karatu da yawa in da a karshe ya samu nasara a matakin karatun izu 60 da tafsiri.

Sai Nusaiba Shuaibu Ahmad daga bangaren mata, wadda ita ma ta zo ta daya a bangaren izu 60, kuma yar asalin jihar Kano ce.

Sama da yara miliyan 26 ne ke fama da karancin ruwan sha a Najeriya - UNICEF

Litinin, 22 ga watan Maris aka yi bikin ranar ruwa ta duniya, yayin da sama da mutum biliyan 1.42 ke fama da karancin ruwan sha a duniya, ciki kuma akwai yara kanana miliyan 450 da ke rayuwa cikin wannan matsala a duniya, in ji Asusun Tallafawa kananan yara na Duniya UNICEF.

Wannan adadi na nufin duk cikin yara biyar akwai daya da ke fama da karancin ruwan da zai biya bukatunsa na yau da kullum.

Yawan irin wadannan yara a Najeriya na da matukar tayar da hankali, inda yara miliyan 26.5 ke rayuwa cikin matsananciyar matsalar ruwa, kimanin kaso 29 cikin 100 na yaran Najeriya ke nan.

Da yake bayani game da wannan rana wakilin UNICEF a Najeriya Peter Hawkins, ya ce "Kananan yara ne suka fi cutuwa daga wannan matsala ta karancin ruwan sha, akwai bukatar a magance ta domin ba su rayuwa mai inganci".

Rahoton na UNICEF ya bayyana yadda yara ke shan wuyar wannan matsala a kasashe 80 a duniya.

Ya ce a gabashi da kuma kudancin Afrika akwai yara sama da kashi 58 cikin dari na adadin wadan nan kasashe.

A tsakiyar Afrika akwai kashi 31, sai Kudancin Asia da ke da kashi 25, a gabas ta tsakiya akwai kashi 23 na yaran da ke rayuwa cikin kamfar ruwan sha.

Yusuf Buhari zai auri Zarah Nasir Ado Bayero?

Yusuf Buhari, ɗa ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai auri Zarah Nasir Ado Bayero, 'yar gidan Sarkin Bichi, bayan sallah mai zuwa.

Wata majiya mai kusanci da fadar Masarautar Bichi ta tabbatar wa BBC cewa ɓangarorin biyu sun haɗu sun tattauna kan soyayyar da ke tsakanin matasan biyu.

Kazalika majiyar, wadda ba ta so a ambaci sunanta, ta ce ɓangaren shugaban Najeriya ne ya tafi wurin iyalan marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero domin neman auren Zarah Nasir Bayero.

"Ɓangaron biyu sun amince tare da tsayar da lokacin bikin zuwa bayan sallah, ta yiwu bayan sallar azumi ko kuma layya," in ji majiyar tamu.

Sai dai majiyar ba ta amsa tambayar BBC kan ko an kai kuɗin gaisuwar iyaye ko na na-gani-ina-so ba kamar yadda yake bisa al'ada.

Wasu majiyoyi sun ce matasan biyu sun haɗu da juna ne a ƙasar Ingila inda Yusuf ya kammala karatunsa na digiri yayin da ita kuma Zarah har yanzu tana ci gaba da nata karatun.

Rabi'u Kwankwaso: Kalli bidiyon tsohon gwamnan Kano kan filayen da ake zargin Ganduje na sayarwa

Tsohon Gwamnan jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya soki lamirin gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje game da shirin gwamnatinsa na karbar rancen naira biliyan ashirin don aiwatar da aikin gina gada a birnin Kano.

Sanata Kwankwaso ya ce ba dai-dai ba ne gwamnati ta ci bashin da zai bar al'ummar da za a haifa nan gaba da dawainiyar biya.

A tattaunawarsa da BBC, tsohon gwamnan Kanon ya ce hakkin gwamnatin tarayya ne ta gina gadar, wadda ta hada birnin Kano da hanyar zuwa Wudil.