A kowacce shekara miliyoyin Musulmai suna azumi tun daga fitowar rana har faduwarta, na tsawon kwanaki 29 ko 30 a cikin watan Ramadan.
A shekarun baya-bayan nan dai Ramadan na fadowa ne a watannin bazara a kusurwar duniya daga arewa, hakan zai janyo ranaku masu tsawo da kuma yanayi mai dumi.
Hakan na nufin cewa wasu kasashe kamar su Norway, mutane za su yi azumi na tsawon sa'o'i 20 a wannan shekarar.
Shin ko wane irin tasiri azumi ke yi a jikin mutum? Dr Lawal Musa Tahir wani kwararren likita da ke asibitin Nizamiye a birnin Abuja, ya lissafa alfanun azumi ga jikin dan adam guda takwas:
- Rage yawan sikari daga jikin dan adam
- Kona kitse
- Rage teba
- Inganta lafiyar zuciya
- Inganta garkuwar jiki
- Tsaftace jiki da hutar da sassan jiki
- Inganta lafiyar kwalkwalwa
- Hana kasala
Rage yawan sukari daga jikin dan adam
A ka'ida dai jikin mutum ba ya shiga yanayin azumi sosai sai an shafe sa'a takwas bayan abinci na karshe da mutum ya ci. Wannan shi ne lokacin da cikin mutum ya gama narkar da abubuwan gina jiki da ya samu daga abincin.
Jim kadan bayan wannan lokacin, jikinmu zai koma wa sikarin da ke adane a hanta da tsokar jikinmu domin samun karfi. Bayan dan lokaci kadan, idan sikarin ya kare, to kitse ne zai koma wuri na gaba da jiki zai iya samun karfi daga gare shi.
Kone kitsen jikin dan Adam
Idan jikin mutum ya fara kone kitse, wannan na taimakawa wajen rage kiba da rage maiko da kuma rage yiwuwar mutum ya kamu da ciwon siga.
Rage teba
Sakamakon kone sukari da kitse a jikin dan adam, hakan na sa nauyi da kibar dan adam ta ragu wadda hakan ce manufar motsa jiki.
Inganta lafiyar zuciya
Masana na cewa mutane da dama kimanin kaso 31.5 da ke mutuwa na mutuwa ne sakamakon cututtuka masu alaka da ciwon zuciya.
Dr Tahir ya ce azumi na inganta lafiyar zuciya kasancewar yana kone kitse sannan ya kawar da teba, al'amarin da ke daidaita sauka da hawan jini.
Inganta garkuwar jiki
Da zarar an kone sukari da kitse kuma an rage teba sannan an samu lafiyar zuciya to dan adam ya kan samu garkuwa da kuzari fiye da lokacin da ba ya azumi.
Ita kuma garkuwa na taimaka wa jiki ne wajen hana kamuwa da wata cuta ko kuma cutar ba za ta yi tasiri a jikin dan adam ba.
Tsaftace jiki da hutar da sassan jiki
Idan aka ci rabin watan Ramadan, jikin mutum yana sabawa da azumi. Hanji da koda da huhu da ma fatar mutum na tsaftace kansu. Sannan sassan jikin da ke aikin tace abinci lokacin da mutum ya ci abincin za su huta ne lokacin azumi.
Inganta Lafiyar kwakwalwa
Kamar yadda motsa jiki yake sanya kwakwalwa ta yi aiki yadda ya kamata, to sakamakon azumi ana iya samun wannan alfanu.
Hana kasala
Idan mutum ya ci abinci sannan ya sha ruwa abin da ke biyo baya a mafi yawan lokaci shi ne kasala. To amma a lokacin azumi babu irin wannan kasala kasancewar ba a ci abinci ba.
Bude baki
To sai dai Dr Lawal Musa Tahir ya ce ya kamata jama'a su yi hattara wajen bude baki. A lokacin da jikin mutum ya fara sabawa da azumi, kitse na raguwa kuma shi ne ke zama sikari a jini.
Dole sai an mayar da ruwan da mutum duk ke rasawa a yayin azumi, in ba haka ba zufa za ta iya janyo rashin ruwa a jiki. Saboda haka dole ne abincin da mutum zai ci ya kasance mai gina jiki.
Ya kara da cewa "Ya kamata a fara amfani da kayan marmari wajen bude baki sannan kuma za a iya amfani da abu mai dumi."
Dangane kuma da mutanen da suke yin dore, Dr Tahir ya ce "akwai matsala idan dai har a ka dauki doren al'ada, inda rumbun ajiya da ke jikin dan adam zai yi kasa kuma hakan na nufin mutum zai galabaita."