A ranar Talata da Laraba ne Musulmai daga sassa daban-daban na duniya suka fara Azumin watan Ramadan.
Wannan nau'in ibada mai matukar muhimmanci na farawa ne da zarar an ga jaririn wata.
Ta yaya aka fara? Ko kimiyya, musamman ilimin taurari za su taimaka wajen lissafi, da samar da maslaha ta dindindin a yayin ganin wata? Shin yaya musulman Afirka ke kallon hakan?
Daga shekara zuwa shekara lokacin Azumin watan Ramadan na sauyawa da kwanaki 11, saboda a kowacce shekara ana daukarsa ne a watan tara na kalandar Musulunci (ana alakanta hakan da lokacin da Annabi Muhammad SAW ya yi hijira daga Makka zuwa Madina) ana kuma amfani da kwanan watan ne da yake da akalla kwanaki 354 ko 355, maimakon kwanaki 365 na Miladiyya.
Saboda haka lokacin na sauyawa daga wata kasa zuwa wata, wani lokacin ma a kasa guda.
Imam Mouhamadou Makhtar Kanté, malamin addinin Musulunci ne a Senegal, ya yi bayani kan muhimmancin watannin addinin Musulunci saboda alakarsu da ibada, ya kuma taba rubuta littafi kan hakan.
Ya shaida wa BBC cewa: "Lokacin ibadar aikin Hajji, da watan Ramadan, da lokacin Ashura da Tasu'a suna da alaka da watannin Musulunci.
"Haka nan lokutan yin sallah suna tafiya ne da fitowa da faduwar rana."
Ta yaya kimiyya za ta taimaka?
Maram Kairé, shi ne shugaban kungiyar masana taurari a Senegal, ya kwashe shekara da shekaru yana kokarin ganin an yi amfani da ilimin kimiyya wajen ganin wata.
Yana aikin hadin gwiwa da malaman addinai a kasar, sannan a ranar Litinin ya gudanar da taron wayar da kai kan ganin wata a birnin Dakar.
"Ilimin taurari, kimiyya ce da aka dade ana amfani da ita a al'adun Larabawa Musulmai. Kimiyya za ta saukaka hanyar samun bayanai.
"Akwai musulmai da ke ganin yana da kyau a yi duban wata idan bukatar hakan ta taso.
Wasu na ganin lissafin masana taurari shi ne kadai hanyar magance matsalar. Ta hanyar ba da bayanai masu alaka da lokaci domin kaucewa kuskuren lokacin ganin wata ta hakan za a kaucewa kura-kurai," kamar yadda ya yi wa BBC karin bayani.
Ya kara da cewa akwai bambanci tsakanin masu duban wata ta hanyar amfani da na'urar hangen nesa.
Sai dai ya kara da cewa, a yanzu amfani da abin hangen nesa ya zama gama-gari.
"Babu abin hangen nesa a zamanin manzon Allah SAW."
Imam Mouhamadou Makhtar Kanté, malami mai wa'azi, ya yi amanna zamanin musulman farko ba su yi nazari a kan ƙididdigar kwanan wata ba.
Ya kara da cewa an yi ce-ce-ku-ce a kan yadda za a gane kwanan wata zuwa tambaya guda biyu: Shin ido ne kadai zai iya ganin jaririn watan, ko kuwa za a yi amfani da lissafin masu ganin watan?
"Yawancin mutane na duban wata da ido ne kamar yadda ya zo a cikin koyarwar Annabi SAW a Hadisai. Sai dai malamai sun yi ittifakin ana yin hakan ne saboda rashin wadanda suke da ilimi a wannan fannin a zamanin manson Allah SAW.
Tun a shekarar 1978 a taron da shugabannin kasashen musulmai suka gudanar, sun yi kiyasin Alkur'ani ya yi magana a kan ilimin ganin wata, hakan zai ba da damar sanin kura-kuran da aka yi domin a gyara.
Misali a kasar Senegal, musulmai daban-daban ne ke bazuwa neman wata.
A wannan shekarar an samu hadin kai tsakanin musulman kasar a ranar Talata, yayin da kwamitin neman wata na Senegal ya ayyana ranar Laraba matsayin wadda za a fara azumin watan Ramadan.
Kungiyar masu ganin wata a Senegal sun yi aikin hadin gwiwa da sauran al'ummar Musulmi da ke neman watan daga Dakar.
BBC ma ta halarci wajen, kuma ba a gano watan ba ta tsohuwar hanyar gargajiya wato amfani da ido ko abin hangen nesa.
Amma duk da haka wasu musulmai na kasar suka yanke shawarar fara azumi ta dogaro da ganin watan da wasu kasashen duniya suka yi.
Can a Congo, an fuskanci matsala wajen ganin wata saboda rashin kyawun yanayi, domin haka sai shugabannin addinin musulunci suka yanke shawarar amfani da ganin watan da kasashen Saudiyya da Qatar suka yi.
"A ko da yaushe akwai kwamiti guda da ake kafawa daga farko zuwa karshen watan Ramadan. Amma a yanzu saboda hayaki mai gurbata muhalli ana matukar shan wuya kafin ganin wata saboda rashin tsaftatacciyar sararin samaniya.
"Amma ana bin kasashe masu karfi kamar Saudiyya da Qatar wajen farawa da ajiye Azumi, " in ji Djuma Twara, sakatare janar na kungiyar musulmi a Congo.
A Faransa kuwa, kungiyar mabiya addinin da babban masallacin birnin Paris, suna amfani da masu ilimin ganin wata domin gane lokacin da za a fara azumin watan Ramadan.
Tun ranar 1 ga watan Afirilu musulman Faransa suka san za a fara Azumi a ranar 13 ga watan Afirilun 2021.
A wannan kasar, ana sanya kimiyya a sahun gaba domin kidayar farawa da sauke Azumi da kuma watanni masu muhimmanci na addinin Musulunci.
Amma a Moroko ana amfani da ido ne wajen ganin wata.
Ma'aikatar harkokin addinin Musulunci da Hubusi, ta sanar da ganin wata da fara Azumin Ramadan a ranar Laraba 14 ga watan Afirilu 2021.
Hakan ya faru saboda rashin ganin watan a ranar Talata kamar yadda kwamitin ganin watan ya bayyana.