BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021

Source: BBC

Ranar Mata ta Duniya: Mata 14 da suka yi fice a arewacin Najeriya

Wasu fitattun mata a arewacin Najeriya da suka taka rawar gani Wasu fitattun mata a arewacin Najeriya da suka taka rawar gani

Yayin da ake bikin Ranar Mata ta Duniya, mun duba fitattun mata a arewacin Najeriya da suka taka rawar gani a ɓangarori daban-daban kama daga shugabanci da siyasa zuwa kimiyya da fasaha da aikin shari'a da likitanci da fafutukar kare haƙƙin mata da dai sauransu.

Amina J Mohammed

Amina J Mohammed ita ce mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya kuma ƴar asalin jihar Gombe ce a arewacin Najeriya.

Kafin riƙe wannan muƙami, Amina J Mohammed ta taɓa zama Ministar Muhalli ta Najeriya inda ta ja ragamar ƙasar kan kare muhalli.

Ta riƙe muƙamai daban-daban a Najeriya a ɓangaren ilimi da walwalar al'umma.

Amina J Mohammed ta zama kamar wata alama ta mace ƴar arewacin Najeriya yadda kullum take sanye da tufafi na gargajiya. Tana ɗaya daga cikin matan da suka yi fice kuma suka zama abin koyi ga mata da dama a ƙasar.

Zainab Bulkachuwa

Zainab Bulkachuwa ita ce mace ta farko da ta zama shugabar kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya.

Ƴar asalin garin Nafaɗa a jihar Gombe, Zainab Bulkachuwa ta yi Cif Majistare a 1985, sannan ta tafi Babbar Kotu a 1987.

Haka kuma ta taɓa rike mukamin Babbar Mai Shari'a ta Babbar Kotun Gombe da mai shari'a a Kotun Daukaka Kara a Abuja.

Zainab Shamsuna Ahmed

Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed ita ce ministar kuɗin Najeriya ƙarƙashin mulkin shugaba Buhari.

Kafin nan ta yi ƙaramar ministar kuɗi kuma ta shugabanci hukumar NEITI.

Ƴar asalin jihar Kaduna, Zainab Ahmed ta riƙe mukamai da dama a Najeriya ciki har da zama darakta a kamfanin zuba jari na Najeriya reshen jihar Kaduna.

Hadiza Bala Usman

Hadiza Bala Usman ita ce shugabar Hukumar Kula da Tasoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya, NPA.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa ta mukamin ne a shekarar 2016.

Hadiza ta yi suna a matsayin mai fafutukar kare haƙƙin mata musamman lokacin da aka sace ɗaliban makarantar Chibok a jihar Borno a Najeriya.

Ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa gangamin BringBackOurGirls wanda ya yi fice sosai a faɗin duniya bayan sace ƴan matan a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Maryam Aloma Mukhtar

Maryam Aloma Mukhtar ta taɓa zama Alƙalin Alƙalai a Najeriya daga shekarar 2012 zuwa 2014.

Ƴar asalin jihar Adamawa, Maryam Aloma Mukhtar ta kasance maced ta farko da ta rike mukamai da dama

Ita ce lauya mace ta farko a arewacin Najeriya kuma Mai Shari'a mace ta farko a Babbar Kotun jihar Kano, kuma Mai Shari'a mace ta farko a Kotun Ƙoli a Najeriya.

Pauline Tallen

Mrs Pauline Kedem Tallen ita ce ministar harkokin mata a Najeriya.

Ƴar asalin jihar Filato, ta taɓa rike mukamin ƙaramar ministar kimiyya da fasaha a gwamnatin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo a shekarar 1999.

Haka kuma, ta taɓa neman kujerar gwamna a jihar ta Filato amma ba ta samu ba.

Ita ce mace ta farko a arewacin Najeriya da ta riƙe mukamin mataimakiyar gwamna.

Sadiya Umar Farouq

Hajiya Sadiya Umar Farouq ita ce minista ta farko da ta rike sabuwar ma'aikatar Jinkai da Ci gaban Al'umma da Kare Afkuwar Bala'i a Najeriya da Shugaba Buhari ya kafa a shekarar 2019.

Kafin nan ita ce kwamishiniyar Hukumar da ke Kula da Ƴan Ci Rani da Ƴan Gudun Hijira.

Ƴar asalin jihar Zamfara, Sadiya Farouq ta taɓa zama Ma'aji ta jam'iyyar APC ta kasa.

Najatu Muhammad

Najatu Muhammad ta kasance ɗaya daga cikin mata ƴan siyasa masu murya a arewacin Najeriya.

Ta tsaya takarar sanata a jiharta ta Kano a shekarar 2007 karkashin jam'iyyar ACN amma ba ta yi nasara ba.

Najatu Muhammad ƴar asalin jihar Kano ce kuma ta yi suna wajen sukar manufofin gwamnati da ba sa amfanar talakawa.

Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe

Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe ita ce mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i.

Ita ce mace ta farko da ta rike wannan mukamin a jihar.

Dokta Hadiza Balarabe likita ce kafin ta shiga harkokin siyasa.

Farfesa Ruqayyatu Rufa'i

Farfesa Ruqayya Ahmed Rufa'i tsohuwar ministar Ilimi ta Najeriya ƙarƙashin mulkin Goodluck Jonathan.

Hajiya Ruqayyatu Rufa'i ta yi ilimi mai zurfi a jami'ar Bayero ta Kano inda ta yi digiri na farko da na biyu. Daga bisani ta tafi Jami'ar West Virginia inda ta yi digirin digirgir.

Farfesa Ruqayyatu ta taka muhimmiyar rawa a ɓangaren ilimin ya mace a jiharta ta Jigawa inda har ta hana amfani da wayoyin salula a makarantun sakandire a jihar.

An nada Farfesa Rukayyatu Rufai a matsayin Kwamishiniyar harkokin Lafiya ta jihar Jigawa daga shekarar 1993 zuwa 1996.

Ta zama Farfesa a shekarar 2003, sannan ta sake rike mukamin Kwamishiniyar Ilimi da Kimiyya da Fasaha a jihar Jigawa.

A shekarar 2010 ne mukaddashin shugaban Najeriya a wancan lokacin, Dr Goodluck Jonathan, ya nada ta a matsayin Ministar harkokin Ilimi ta kasar.

Zaynab Alƙali

Farfesa Zainab Alkali na ɗaya daga cikin marubuta mata yan arewacin Najeriya da suka yi fice wurin rubutu da Ingilishi.

Littafanta sun yi suna sosai a Najeriya kuma ana karanta su a makarantun Sakandire.

Rubuce-rubucenta sun shafi yadda mata ke rayuwa a arewacin Najeriya da ilimin ƴa mace da dai sauransu.

Ana ganin Farfesa Zaynab Alkali a matsayin mace marubuciyar zube ta farko a arewacin Najeriya.

Aishatu DukkuAishatu Dukku ƴar siyasa ce wadda ta taba rike muƙamin ministar Ilimi a Najeriya lokacin mulkin Umaru Musa Ƴar'adua.

Haka kuma, ƴar majalisa ce a majalisar dokokin ƙasar inda ta ke wakiltar mazaɓar Dukku da Nafaɗa a jihar Gombe.

Hajiya Aishatu na taka muhimmiyar rawa a ɓangaren ilimin ƴaƴa mace da inganta rayuwar mata masu karamin ƙarfi da ci gaban matasa.

Aishatu Dahiru Ahmed (Binani)

Aishatu Dahiru Ahmed wadda ake yi wa laƙabi da Binani ƴar majalisar datiijan Najeriya ce ƙarkashin jam'iyyar APC.

Ƴar asalin jihar Adamawa, Aishatu Binani ta taɓa zama ƴar majalisar wakilai ƙarkashin jam'iyyar PDP tsakanin shkekarar 2011 zuwa 2015.

Sanata Aishatu ƴar kasuwa ce kuma shugabar kamfanin Binani Nigeria Limited.

Binta Masi Garba

Binta Masi Garba ƴar siyasa ce kuma yar kasuwa a arewacin Najeriya.

Ta taɓa zama sanata sannan ta yi shugabar jam'iyyar APC a jiharta ta Adamawa. Ita ce mace ta farko da ta riƙe wannan mukami a babbar jam'iyya a Najeriya.

A zaɓukan 2015, ta kasance mace daya tilo yar arewa a majalisar dattijan kasar.