BBC Hausa of Tuesday, 23 March 2021

Source: BBC

Ranar Ruwa Ta Duniya: Hanyoyi biyar da za ku kauce wa kamuwa da cututtuka ta ruwan sha

Rahoton UNICEF wai yara miliyan 450 na fuskantar karancin ruwan a rayuwa Rahoton UNICEF wai yara miliyan 450 na fuskantar karancin ruwan a rayuwa

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef, ya ce mutum biliyan daya da miliyan arba'in da biyu ne suke rayuwa a yankunan da ake fuskantar matsanancin karancin ruwan sha mai inganci a duniya.

Wani sabon rahoto da asusun ya fitar ya ce cikin wadannan mutane akwai yara miliyan 450 da ke fuskantar karancin ruwan yin mu'amalar yau da kullum.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake bikin ranar Ruwa Ta Duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a kowacce shekara saboda hakan.

Najeriya na daga cikin kasashe 80 da rahoton UNICEF ya ambato fiye da yara miliyan ashirin da shida ne ke fama da karancin ruwan shan, wato kashi 29 cikin dari na yaran da ke kasar.

Wannan karancin ruwan sha na jefa ba yara kadai cikin hadarin harbuwa da cututtuka da kuma kuncin rayuwa ba har da manya. Rashin ruwa mai tsafta na haddasa cututtuka kamar amai da gudawa, da ciwon ciki, da kuraje da sauransu.

Ko wadanne hanyoyi ya kamata a bi domin tsaftace ruwan sha domin kauce wa kamuwa da cutuka? Dakta Salihu Ibrahim Kwaifa, kwararren likita ne a Abujar Najeriya, ya zayyano hanyoyi biyar da za a tsaftace ruwan sha domin kauce wa kamuwa da cutuka.

1 Wajen da aka debo ruwan:

Ya kamata wurin da ake debo ruwan - rijiya ko famfo - ya kasance mai tsafta. A tabbatar ruwan da yake fitowa daga wadannan wurare mai tsafta ne bai sauya launi ko dandano ko kamshi ba.

2. Dafawa:

Domin kauce wa kamuwa daga cututtukan da ake samu a ruwan da ake amfani da shi a bukatun yau da kullum, yana da muhimmanci a tafasa ruwan ta yadda dukkan kwayoyin cutar da yake dauke da su za su mutu - ya zamo mai tsaftar da za a iya sha.

3. Tacewa:

Tace ruwan da aka dafa bayan ya huce yana da muhimmanci, ana iya tacewa da wani kyalle mai tsafta ko abin tace ruwa na zamani da ake kira water filter, sannan ba lalllai sai ruwan da aka dafa ake iya tacewa ba.

Abu mai muhimmanci shi ne tace ruwan tana kwashe dattin da ruwan ke dauke da shi.

4. Adanawa:

Adana ruwa cikin mazubi mai kyau da tsafta yana hana cututtuka shiga ruwan. Ko dai tulu, ko kwarya, ko bokitin da ba a shiga bandaki da shi, ko jarkar da ake zuba shi.

A kuma tabbatar mazubin yana da murfin da za a rufe ruwan da shi saboda gudun shigar datti ko wani abin cutarwa.

5. Tsaftar hannu:

Ya kasance muna yawan wanke hannunmu da sabulu domin tabbatar da tsaftarmu kafin taba ruwan da aka tsaftace daga cututtuka.

Saboda idan hannu akwai datti a jikinsa aka kuma yi amfani da shi ko kama moda ko abin diban ruwan aka sanya ciki zai janyo cutuka shiga ruwan.