BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021

Source: BBC

Rashin doka na janyo wa Najeriya asarar biliyoyi

Majalisar wakilan Nijeriya a Abuja Majalisar wakilan Nijeriya a Abuja

Majalisar wakilan Nijeriya ta ce rashin dokokin rabon albarkatun kasa sun sa suna dibarsa suna tafiya da shi ba ba tare da an yi rabo ba.

Domin yin gyra Majalisar wakilan ta shirya wani zama domin lalubo hanyoyin magance matsalar.

Ta ce wasu daga cikin dokokin tun daga shekarar 1970 kuma baa yi mu su kykkyawan gyra ba.

Onarabul Abdullahi Mahmud Gaya, wanda shi ne shugaban kwamitin albarlatun man fetur na aka tace a Majalisar ya ce rashin gyra dokokin na janyo wa kasar asarar biliyoyin naira.

Ya kuma ce sun dukufa wajan gyra dokokin ta hanyar shigar da bangaren makamashin iskar gas cikin yarjeniyoyin hakar man fetur a Najeriya.

Nijeriya kasa ce mai dimbin arzikin iskar gas amma ta fi dogara da man fetur wajan samun kudaden shiga