A baya-bayan nan, an samu ƙaruwar kai wa ƴan sanda hare-hare a yankin jihohin Ibo da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Duk da cewa ƙasar na fama da matsalolin tsaro na garkuwa da mutane da ɓarayin daji da dai sauransu musamman a yankin arewa, wani sabon salo ya fara kunno kai a yankin kudu.
Maharan da kawo yanzu ba a san ko su wane ne ba na kai harin ne a jihohin Abia da Imo da Ebonyi da Imo da Anambra.
Ko a ranar Litinin ɗin da ta gabata, rahotanni sun bayyana cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari wani ofishin ƴan sanda a jihar Imo.
Rahotannin sun bayyana cewa an kai hari ne a hedikwatar ƴan sanda da ke unguwar Isiala Mbano a Umuelemai inda wani jami'in ƴan sanda ya bayyana cewa maharan sun ji wa ɗan sanda ɗaya rauni sannan suka ƙona wasu takardu na amfani.
Ya bayyana cewa sun zarce wurin ajiye bindigogi ne a ofishin kuma da ba su samu bindiga ko ɗaya ba ne suka kama ƙona takardun.
Ko a jihar ta Imo kawai, wannan ne hari na biyu a ƙasa da wata guda da aka kai wa jami'an ƴan sanda.
Haka ma a jihar Abia, wasu ƴan bindiga sun kashe wasu jami'an ƴan sanda a ƙaramar hukumar Ohafia ta jihar Abia ranar Litinin, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
Sai dai a wannan karon ƴan sandan na duba motoci ne a kan titi lokacin da ƴan bindigar suka far masu tare da ƙwace bindigoginsu a garin Abiriba.
Ire-iren waɗannan hare-haren suna nema su zama ruwan dare a yankin na kudancin Najeriya.
Ya masana ke kallon lamarin?
Farfesa Muhammad Kabir Isa na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, masanin harkokin tsaro a Najeriya ya bayyana cewa ba komai ne ya janyo wannan ba illa rashin kula da rundunar ƴan sanda da gwamnatin Najeriya ke yi.
Ya ce gwamnati ta fi mayar da hankali kan sauran rundunonin tsaro kan ƴan sanda.
"A Najeriya gwamnati ta fi kulawa da Hukumar Fasa ƙwabri fiye da rundunar ƴan sanda, ba tun yau ba. Gwamnatocin da suka shuɗe ma haka suka yi watsi da ƴan sanda.
"Kuma illar hakan muke gani, shi ya sa ba sa iya yin komai har ake iya kai masu hari su kasa kare kansu," a cewarsa.
Ya kuma ce ba yau aka fara ganin irin wannan matakin na satar makamai ba a Najeriya, kusan salon da ƙungiyar Boko Haram ma ta ɗauka kenan a lokacin da ta fara ayyukanta a arewa maso gabashin Najeriya.
Farfesa Muhammad Kabir ya ce hasashensu shi ne ƴan kungiyar IPOB ta ƴan aware ne ke kai waɗannan hare-haren.
Ya ce ƙungiyar ta daɗe tana shirin ɓallewa daga Najeriya kuma wannan hare-hare da ake kai wa ƴan sanda tare da sace makamansu kamar nuna ƙwanjinta take yi.
Ya ce dole ne gwamnati ta zage damtse ta ƙwaƙulo su sannan ta yaƙe su a duk inda suke kafin su haifar da yaƙin da zai fi ƙarfin ƙasar.
"Ina ma iya cewa gwamnati ta makara, saboda an yi sake tun farko. Abin da har yanzu aka baro Najeriya a baya shi ne batun leƙen asiri. Ai ba a iya tsaron ƙasa ba tare da leƙen asiri ba," a cewarsa.
Ya ce duk wata ƙasa da ke ji da kanta a fannin tsaro tana da kafofin leƙen asiri a gida da waje.
Haka kuma, Farfesa Muhammad kabir ya ce dalilin da ya sa suke da ƙwarin gwiwar kai wa ƴan sanda hari har su kashe su ko su ƙone ofishinsu saboda sun san jami'an ƴan sandan ba su da ƙwarewa a aiki.
"Akwai jami'an ƴan sanda da suka daɗe a aiki amma ba a taɓa yi musu wani horo na musamman ba, wannan ma kawai ya isa ya shafi tsaro a ƙasar nan," in ji shi.
Ya ce jami'an tsaron Najeriya ba su da wani albashi mai tsoka balle su samu karsashin aiki.
Farfesan ya ce cin hanci da rashawa ma na cikin abubuwan da suka janyo taɓarbarewar tsaro a Najeriya.
Ya ce idan gwamnati za ta gyara waɗannan matsalolin ana iya yi wa tufkar hanci.
Najeriya dai ta daɗe tana fama da matsalolin tsaro iri-iri, amma a iya cewa al'amarin na ƙara ta'azzara.
Masana harkokin tsaro na ganin cewa nan da ƴan wasu shekaru, kasar na iya shiga hali ha'ula'i na tsaro musamman yadda akwai rarrabuwar kawuna tsakanin ƴan ƙasar - wato ƴan kudu da ƴan arewa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ɗauki matakai da dama na daƙile matsalolin tsaro a ƙasar, kamar sauya hafsoshin tsaro da iƙirarin fitar da kuɗadensayen kayan yaƙi. Sai dai wasu ƴan ƙasar na ganin hakan bai isa ba.
Har yanzu akwai matsalolin garkuwa da mutane da ɓarayin daji da satar ɗalibai daga makarantunsu da wasu gungun mutane ke yi don kuɗin fansa.
Yanzu da wannan sabon salon na kai wa ƴan sanda hari, ko wace hanyar gwamnati za ta bullo da shi don tunkarar matsalar ka'in da na'in?