BBC Hausa of Tuesday, 13 April 2021

Source: BBC

Real Madrid za ta dogara da Courtois idan ta je Anfield

Thibaut Courtois, golan Real Madrid, ya fuskanci Liverpool sau shida Thibaut Courtois, golan Real Madrid, ya fuskanci Liverpool sau shida

Ranar Laraba Real Madrid za ta ziyarci Liverpool, domin buga wasa na biyu na quarter finals da za su kece raini a Anfield.

A wasan farko da suka yi ranar Talata a Spaniya, Real ce ta yi nasara da ci 3-1 a gasar ta zakarun Turai.

Liverpool na bukatar cin kwallo biyu domin ta kai zagayen daf da karshe, sai dai golan Real Madrid, Thibaut Courtois ba a taba zura masa kwallo biyu ba a Anfield.

Mai tsaron ragar tawagar Belgium ya fuskanci Liverpool sau shida, wanda ya yi nasara a karawa hudu da canjaras daya aka doke shi wasa daya tal.

Sau hudu ya je Anfield filin da ba a zura masa kwallo biyu a raga BA, wanda ya yi nasara da ci 2-1 sannan karawa uku suka tashi canjaras da ya kama gola.

A Oktoban 2015, Courtois bai buga karawar da Chelsea ta karbi bakuncin Liverpool ba a Stamford Bridge a wasan da Philippe Coutinho ya ci biyu da kungiyar Anfield ta ci 3-1.

Haka kuma bai yi wa Chelsea karawa ta biyu ba a Anfiled da suka tashi kunnen doki 1-1, wanda Eden Hazard ne ya ci wa kungiyar Stamford Bridge kwallon a fafatawar.

A kakar 2014/15 Chelsea ta kara da Liverpool gida da waje, inda suka yi 1-1 a Anfield a wasan daf da karshe a Caraboa Cup.

A wasa na biyu kuwa a Landan kungiyoyin sun tashi karawar ba ci wato 0-0, inda Courtois ya tsare ragar Chelsea.

Courtois wanda ya koma taka leda a Real Madrid a kakar 2018 zai ziyarci Anfield ranar Laraba, kuma idan ya sa kokari kamar yadda ya yi a baya, Real za ta iya kai wa daf da karshe a bana.

Kuma idan har Real ta fitar da Liverpool, za ta fuskanci Chelsea kenan tsohuwar kungiyar Courtois wadda ta ci FC Porto 2-0 a wasan farko a quarter final.