BBC Hausa of Wednesday, 17 March 2021

Source: BBC

Real ta kai quarter finals karo na 36 a Champions League.

Karim Benzema ya ci kwallo daya Karim Benzema ya ci kwallo daya

Real Madrid ta yi nasarar doke Atalanta da ci 3-1 a wasan zagaye na biyu a Champions League da suka fafata ranar Talata a Alferedo Di Stefano.

Real ta ci kwallayen ta hannun Karim Benzema da Sergio Ramos, sannan Marco Asensio ya ci na uku, ita kuwa Atalanta ta zare daya ta hannun Luis Muriel.

A wasan farko da suka fafata a Italiya ranar 24 ga watan Fabrairu, Real ce ta yi nasara da ci 1-0, jumulla ta kai zagayen gaba da kwallo 4-1 kenan.

Real wadda ta lashe Champions League hudu a kaka biyar tsakanin 2014 zuwa 2018 ta kasa zuwa wannan matakin a kaka biyu da ta buga da Ajax da Man City suka yi waje da ita.

Wannan ne karo na 36 da Real ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a Champions League, wadda ke biye da ita a tarihi ita ce Bayern Munich da 30.

Kuma Zinedine Zidane ya yi nasara lashe wasa 30 a karawa 49 a Champions League - Josef Heynckes ne keda wasa 42 da kuma Pep Guardiola mai karawa 48 da suka ci wasa 30 a karancin buga gasar.

Kawo yanzu mai tsaron baya, Roberto Carlos shi ne kan gaba a cin kwallo a gasar zakarun Tura da 16, sai kyaftin Sergio Ramos mai 15 a jerin masu tsaron baya da suke kan gaba a cin kwallaye.

Real Madrid wadda aka fitar a Copa del Rey tana ta uku a kan teburin La Liga da tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona ta biyu mai tazarar maki hudu tsakaninta da Atletico Madrid ta daya a gasar bana.