BBC Hausa of Tuesday, 2 March 2021
Source: BBC
Real Madrid ta buga karawar Champions League ta 100 a fafatawar zagaye na biyu, inda ta doke Atalanta da ci 1-0 ranar Laraba.
Real ta ci Atalanta kwallo ta hannun Ferland Mendy saura minti hudu a tashi daga karawar.
Atalanta za ta ziyarci Real Madrid domin buga wasa na biyu ranar 16 ga watan Maris a Estadio Alfredo Di Stefano a Spaniya.
Madrid ta kawo wannan matakin ne a gasar bana, bayan da ta yi ta biyu a rukuni na biyu, kuma karon farko da za ta kara da Atalanta a gasar ta Champions League a tarihi.