BBC Hausa of Sunday, 30 May 2021

Source: BBC

Rikicin Belarus: Putin ya soki Tarayyar Turai a taronsa da Lukashenko

Shugaban Rasha Vladimir Putin (dama) Shugaban Rasha Vladimir Putin (dama)

Shugaban Rasha ya yi watsi da fushin da kasashen Turai ke nunawa kan tilastawa jirgin Ryanair sauka a babban birnin Belarus domin a kama wani dan jarida da budurwarsa domin yana adawa da gwamnatin kasar.

Yayin wata ganawa da ya yi a birnin Sochi da takwaransa na Belarus Alexander Lukashenko, Mista Putin ya tabo abin da ya kira "kwararar damuwa da bin zuciya."

Tarayyar Turai tuni ta bukaci kamfanonin da ke jigilar fasinja na yankin yammacin Turai da su kauracewa sararin samaniyar Belarus.

Sun kuma bkaci a sako Roman Protasevich da budwarsa Sofia Sapega.

Wadannan mutum biyun na cikin wani jirgin sama ne da ya taso daga birnin Athens zuwa Vilnius ranar Lahadi, inda hukumomin Belarus su ka aika da wani jirgin yaki a cikin kasar ta Belarus domin ya raka jirgin fasinjar zuwa Minsk babban birnin kasar Belarus wa saboda sun gano an dasa bam a cikinsa.

Sai dai daga baya an gano cewa yaudara ce kawai, babu wani abin fashewa a cikin jirgin.

A cikin jirgin akwai Mista Protasevich mai shekara 26, da buduwarsa Ms Sapega mai shekara 23, wadda ke karatun fannin shari'a a jami'a kuma 'yar asalin kasar Rasha ce. An kama su yayin da fasinjoji ke sauka daga jirgin.

Mista Protasevich shi ne editan jaridar Nexta, wadda jarida ce ta 'yan adawar kasar Belarus da ke da wani shafin mai farin jini a manhajar Telegram.

Y abar Belarus tun 2019, kuma a yanzu yana zaune ne a matsayin dan gudun hijira a kasar Lithuania.