BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

Rikicin Chadi: Abin da ya sa sojoji suka ki yin sulhu da 'yan tawaye

Sojojin Chadi sun karbi mulki tun bayan mutuwar shugaba Idris Deby Sojojin Chadi sun karbi mulki tun bayan mutuwar shugaba Idris Deby

Majalisar sojin Chadi ta yi watsi da tayin tsagaita wuta da 'yan tawaye da take yaki da su, tun bayan mutuwar ba-zata da Shugaba Idriss Deby ya yi.

Sojojin sun karbi mulki tun bayan kashe Mr Deby a artabu da 'yan tawaye.

A yanzu sojojin, wadanda dan Mr Deby ke jagoranta, sun ce za su ci gaba da mulki nan da watanni 18.

Sai dai 'yan siyasa da kuma 'yan tawaye sun bayyana abin da sojojin suka yi a matsayin juyin mulki.

Rundunar sojin Chadi ta sanar da cewa Mr Deby, mai shekaru 68, ya samu raunuka a yaki da 'yan tawaye jim kadan bayan ya lashe zabe.

An yi arangamar ne a arewacin Kanem.

'Yan tawayen da ake kira Front for Change and Concord in Chad (FACT) sun fito ne daga arewaci a ranar zabe inda suke bukatar a kawo karshen shekaru 30 na mulkin Mr Deby.

Kuma a ranar Asabar da ta wuce ne suka ce a shirye suke a yi sulhu da su, amma ba za su yi mubaya'a ga juyin mulkin da ya kawo dan Idris Deby wato Janar Mahamat Deby kan mulki ba.

  • Su waye 'yan tawayen Chadi, kuma me suke so?
  • Mahamat Idriss Déby Itno: Abin da ba ku sani ba kan ɗan Idriss Deby wanda ya zama shugaban Chadi
Amma daga baya majalisar sojin ta fitar da sanarwar cewa ba za ta tattauna da 'yan tawayen da take yaki da su ba.

"A yanayin da muke cikin yakin da ke barazanar wargaza zaman lafiya a Chadi da ma makwabtanta, ba lokaci ba ne na tattaunawa da duk wanda ba ya bin doka," a cewar mai magana da yawun majalisar soji Azem Bermendao Agouna.

"Ƴan tawaye ne kuma a kan haka ne muke kai musu hari. Kawai muna yaki ne ba wata magana."

Mr Agouna ya ce wasu daga cikin yan tawayen sun tsallaka Jamhuriyar Nijar. A kan haka ne ya bukaci hukumomi a can su kama su domin yi musu hukunci.

Ya kara da cewa shugaban FACT Mahamat Ali ya shirya aiwatar da laifukan yaki a Libya, inda mayakansa ke da yawa.

An samar da kungiyar 'yan tawayen a shekarar 2016 da nufin kifar da gwamnatin Chadi, kuma tana cikin kungiyoyin da ake yaki da su a Libya.

A yanzu majalisar sojin na fuskantar matsin lamba kan bukatar mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya ba tare da bata lokaci ba.

Kwamitin tsaro da zaman lafiya na Tarayyar Afrika ya nuna damuwa kan karbe mulki da sojoji suka yi, yayin da Faransa da manyan kasashen Afrika ke kira da a samar da gwamnatin hadin gwuiwa da za ta kunshi fararen hula da sojoji.

An binne Mr Deby a ranar Juma'a da ta gabata a wata jana'izar ban girma da ta samu halartar dubbai da suka hada da shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Mr Deby ya shiga aikin soji a shekarar 1990 bayan fada da gwamnatin wancan lokacin.

Kuma yana da tsohuwar alaka ta kut-da-kut da Faransa da sauran kasashen Yamma, a yakin da suke yi da kungiyoyin da ke yankin Sahel.


Karin labarai kan kasar Chadi:

  • Tarihin marigayi shugaban Chadi Idris Deby
  • Hotunan jana'izar tsohon shugaban Chadi Idriss Deby