BBC Hausa of Friday, 9 April 2021

Source: BBC

Sai a Faransa za a tantance gwani tsakanin Bayern da PSG

Kylian Mbappe ne ya fara ci wa PSG kwallo minti uku da fara Kylian Mbappe ne ya fara ci wa PSG kwallo minti uku da fara

Paris St Germain ta je har Jamus ta doke Bayern Munich da ci 3-2 a wasan farko fafatawar quarter final a Champions League da suka kara ranar Laraba.

Kungiyoyin biyu sun kara a bara a wasan karshe da Bayern ta yi nasara da ci 1-0 ta lashe Champions League.

Sai dai gumurzun bana ya kayatar matuka ta yadda 'yan wasa suka nuna hazaka da kwarewar murza leda, inda aka haska futalar tamaula na kafar matasa.

Kylian Mbappe ne ya fara ci wa PSG kwallo minti uku da fara tamaula daga baya Marquinho ya kara na biyu.

Bayern ta zare kwallo daya ta hannun tsohon dan wasan PSG, Eric Maxim Choupo-Moting tun kan hutu.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne kungiyar Jamus ta farke na biyu ta hannun Thomas Muller.

Daga baya ne Mbappe ya kara na uku kuma na biyu da ya ci a wasan na hamayya a Jamus.

Wannan nasarar mahimmiya ce ga koci Mauricio Pochettino a gasar Turai, bayan da ya je Spaniya ya ci Barcelona 4-1 a wasan farko zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a Champions League na bana.

PSG ta doke Bayern wacce ta yi wasa 19 a jere ba a doke ta ba da cin 18, rabon da ta yi rashin nasara tun 3-1 da Liverpool ta casa ta ranar 13 ga watan Maris din 2019.

Ranar 13 ga watan Afirilu Paris St Germain za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasa na biyu a Quarter finals.