Yanzu idanu sun koma kan mataimakiyar shugaban kasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan bayan da shugaban kasar John Magafuli ya rasu a ranar Laraba sakamakon ciwon zuciya a wani asibiti da ke birnin Dar es Salaam.
Haka kundin tsarin mulkin Tanzania ya tanada, a rantsar da Samia Suluhu Hassan a matsayin sabuwar shugabar kasa, inda za ta karasa sauran wa'adin shekara biyar din da Magafuli ya fara a bara.
"Lokacin da ofishin shugaban kasa ya zama babu kowa ciki sakamakon mutuwar da ya yi, to za a rantsar da mataimaki ne kai tsaye a wannan lokacin, ya karasa sauran wa'adin shekara biyar din da aka tsara," in ji kundin tsarin mulkin Tanzania.
Idan aka rantsar da Samia Suluhu Hassan a matsayin shugabar kasar, za ta zama mace ta farko da ta rike mukamin, kuma mace ta biyu da ta taba zama shugabar wata kasa a yankin gabashin Afrika.
Wace ce Samia Suluhu Hassan?
Samia Suluhu Hassan ita ce mataimakiyar shugaban kasar Tanzania a yanzu, kuma an haife ta ne a ranar 27 ga watan Janairun 1960.
Mama Samia Suluhu Hassan kamar yadda mafi yawan mutane ke kiranta, 'yar asalin yankin Zanzibar ce mai 'yanci, wanda kashi 99 cikin 100 na mazaunansa Musulmai ne.
Ta karanta ilimin kididdiga a cibiyar tsare-tsaren kudi da ke Zanzibar daga baya ta kammala karatunta a Jami'ar Mzumbe a shekarar 1986, sannan ta yi difloma a al'amuran gudanarwar jama'a.
Ta kuma halarci jami'ar Manchester da ke Ingila inda ta karanci Ilimin tattalin arziki a 1994.
A 2015 ta zama mataimakiyar shugaban kasar, kuma mace ta farko da ta rike wannan matsayi a tarihin Tanzania.
Gabanin haka ta taba rike mukamin ministar cikin gida karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa, sannan kuma ta yi aiki a karkashin gwamnatin Zanzibar a wani matsayi na daban.
Hajiya Samia Suluhu Hassan ba ta cikin rabe-raben da ake fama da shi a jam'iyyarsu mai mulki ta Chama Cha Mapinduzi (CCM).
Kamar yadda wasu masu sharhi kan al'amuran siyasa ke fada da magiya bayan Magafuli da ma wasu mabiya addinin Kirista masu kishin kasa suna adawa da maye gurbin marigayi John Magafuli da za ta yi.
Sai dai wasu rahotanni na cewa tana samun goyon bayan wani bangare daga cikin mambobin jam'iyyarta musamman magiya bayan tsohon shuagaban kasar Jakaya Kikwete, musamman wadanda suke daga yankin Musulmai.
Samia Suluhu Hassan na da miji mai suna Hafidh Ameir tun 1978, kuma suna da 'ya daya da yara maza uku.
Cikin 'ya'yanta hudu, 'yarta Mwanu Hafidh ita ce kawai ta gajeta, wadda a yanzu take a matsayin mamba a majalisar wakilai ta Zanzibar.
A tarihin Tanzania, ba su taba samun shugaban kasa daga yankin Zanzibar ba.