BBC Hausa of Wednesday, 5 May 2021

Source: BBC

Samia Suluhu Hassan: Yadda salon mulkin sabuwar shugabar Tanzania ke sauya alkiblar kasar

Mutumin da ta gada John Magufuli ya yi fice kan yadda yake fitowa ya bayyana ra'ayinsa kan abubuwa da dama yayin da sabuwar shugabar Tanzania ta kasance tana da nutsuwa.

Yayin da ya kasance mutum mai yawan janyo ce-ce-ku-ce, Shugaba Samia Suluhu Hassan ta ba da karfi kan sasantawa.

Magufuli mutum ne mai mulkin kama karya sai dai magajiyarsa Samia ta kasance tana bin tsarin yin tafiya da kowa.

Ƙasa da wata biyu tun mutuwar tsohon Shugaba Magufuli mai shekara 61 amma mataimakiyarsa wadda aka rantsar a matsayin shugabar kasa jim kadan bayan mutuwarsa, da alama salon mulkinta ya banbanta da nasa.

Samia ta kawo wani salo na daban kama daga kan yadda take yaƙi da annobar korona zuwa batun ƴancin kafafen watsa labarai ko ma hulɗa da ƴan hamayya da kuma yadda take gabatar da jawabanta cikin nutsuwa da iko.

Sai dai shugabar da alama, ba ta jin daɗi idan ana kwatanta ta da tsohon shugaban sannan ta nuwa ɓacin ranta game da yadda ƴan majalisar Tanzania suke banbanta ta da Magufuli.

"Magufuli da Samia, a zahiri ɗaya suke. Ina bibiyar muhawarar kuma dole na ce wannan sam ba zai amfani ƙasarmu ba," kamar yadda ta faɗa wa ƴan majalisar wata ɗaya bayan rantsar da ita.

Amma "abu ne mai kamar wuya a ce ba za a yi haka ba," a cewar wani ɗan jarida Jesse Kwayu, yana mai cewa akwai banbanci sosai tsakaninsu.

"Mace ce mai hangen nesa, ta san hanyoyin da suka kamata na isar da saƙo da kuma yin gyara."

Karon farko da ta tsaya kan mumbari a matsayin shugabar kasa, irin kalaman da ta yi amfani da su sun nuna salon shugabancinta daban yake. Salo ne da Tanzania bata taba gani ba tun zamanin Magufuli da aka yi wa laƙabi da "Bulldozer" ya hau kan mulki a 2015.

Babban editan kamfanin yada labarai na Jamhuri Deodatus Balile ya ce ta gabtaar da jawabinta ba tare da inda-inda ba kamar yadda wasu kan yi.

"Ta fahimci cewa ƴan Tanzania ba za su iya rayuwa a killace ba kuma dole ne mu kasance cikin wani tsari sannan mu duba wasu batutuwa a matsayin wani bangare na duniya,"

Babban abin da ya banbanta ta da tsohon shugaban shi ne yadda take tafiyar da yakinta na annobar korona.

Rigakafi da kullen korona?

Magufuli ya soki gargadin da aka rika yi a duniya game da annobar korona da kuma irin barazanar da ke tattare da ita kuma ya ki yadda a kai alluran rigakafin cutar zuwa kasar. Akwai lokacin ma da ya sanar cewa an ci galaba kan cutar saboda ruwan addu'oin da aka yi a Tanzania.

Babu wata sahihiyar kididdiga kan mutanen da suka kamu da cutar ko kuma suka mutu sanadinta a Tanzania saboda gwamnatin Magufuli ta dakatar da fitar da bayanan mutanen da suka kamu tun Mayun bara.

Cikin mako uku da karɓar mulki, ta kafa kwamitin kwararru domin ya ba ta shawara kan halin da ake ciki game da annobar korona a kasar da kuma irin matakan da ya kamata a dauka don kare ƴan ƙasar.

An kuma ganta sanye da takunkumi wani abu da Magufuli bai taɓa yi ba duk da cewa a lokacin tana wata ziyara ne a Uganda ba wai a Tanzania ba ne.

Kawo yanzu, babu wasu sabbin manufofi da kwamitin kwararrun ya bijiro da su na yaƙi da cutar.

Mutane da dama sun ƙagu suga yadda za ta tafi da batun rigakafin cutar ganin yadda aka samu bullar wasu sabbin nau'ikan cutar korona a wasu sassan duniya.

Mutane kuma na jiran ganin ko za ta duba yiwuwar sa dokar kulle da hana fita a matsayin hanyoyin dakile yaduwar cutar, lamarin da Magufuli ya yi watsi da shi.

Irin wadan nan matakan za su shafi miliyoyin talakawan ƙasar har da ƴan kasuwa masu samun goyon bayan jam'iyya mai mulki ta Chama Cha Mapinduzi.

Idan har tana son bin wannan tsarin, toh akwai bukatar Shugaba Samia ta iya gamsar da yan kasar cewa daukar irin matakan abu ne da zai amfane su.

Shugaba Samia ta fara yin fice ne a 2014 lokacin da aka zabe ta a matsayin mataimakiyar shugabar majalisar tsarin mulki da aka dorawa alhakin sake fasalta kundin tsarin mulki.

Ta zama mace mai nutsuwa kuma jagora mai iya banbance tsakanin ra'ayoyi da maganganun yan hamayya," in ji mai sharhi kan siyasar.

Kokarinta na son jin ra'ayoyi daban-daban ya nuna yadda take bai wa aikin jarida yanci.

Gwamnatin Magufuli na da alhakin rufe kafafen yada labarai sannan an zarge ta da cin zarafi da kuma kulle yan jarida. Wasu yan siyasa da masu fafutuka da suka fito fili suka soki Magufuli na cikin wadanda gwmanatin Magufuli ta tsare.

Amma ana ganin Shugaba Samia na ba da damar tafka muhawara.

Tattaunawar sulhu

Ta umarci ma'aikatar yada labarai ta soke matakan da aka dauka a baya cewa kada gwamnati ta bai wa mutane damar fadar cewa muna takaita yancin aikin jarida".

Shugabar ta kuma tuntubi yan hamayya da nufin tattaunawa da su kan yadda za su tafiyar da harkokinsu na siyasa domin ci gaban kasar".

Kuma tuni ta yi suna saboda gudanar da tattaunawar sulhu bayan ziyarar da ta kai wa jagoran yan hamayyar kasar Tundu Lissu a asibiti cikin 2017 bayan da aka harbe shi a wurare da dama a wani yunkurin halaka shi.

Ita kadai ce jami'ar gwamnatin da ta yi haka.

Ana kuma sa ran Shugaba Samia ba za ta dauki tsauraran matakai ba kamar Magufuli kan kamfanonin kasashen waje da ke gudanar da harkokinsu a Tanzania.

A 2017, kamfanin hakon ma'adinai Acacia reshen kamfanin Canada Barrick Gold, ya fuskanci tarar $190bn kan wasu kudade da gwamnati ta ce ana binsa duk da cewa ya musanta yin ba dai-dai ba.

Barrick ya yi kokarin rage kudin a wani bangare na sulhu da gwamnati da ya hada da raba tattalin arzikin a gaba.

Magufuli ya kuma takaita wa yan kasuwar yankin shiga kasuwannin Tanzania tare da tsaurara matakan hana shigo da kayayyaki cikin kasar daga Kenya.

A cewar Shugaban kungiyar masu kamfanoni abin da ta sa a gaba shi ne habaka hannun jari da bunkasa kasuwanci.

"Game da kamfanoni masu zaman kansu, mun kagu mu ga ta janyo yan kasuwa cikin tsare-tsaren gwamnati na gina Tanzania."

Shugaba Samia za ta kai ziyara wata kasar a karo na biyu inda za ta je Kenya cikin mako bakwai da ta kasance kan mulki. Da yake daganta hakan ga bulaguro 10 da Magufuli ya yi zuwa wasu kasashen cikin shekara 6 da ya yi kan mulki, Mista Kwayu yana da kwarin gwiwar cewa sabuwar shugabar za ta yi kokari wajen inganta hulda da kasashen waje.

"Ina da tabbacin za a sake shigar da Tanzania harkokin da suka shafi duniya." a cewarsa. "Za ta shiga batutuwan da suka shafi warware rikici sannan za ta samu kyakkyawan wakilci a wurare kamar Majalisar Dinkin Duniya."

A ganinsa, salon mulkin Shugaba Samia ba wai bata sunan gwamnatin da ta wuce ba ne wadda ta kasance a cikinta.


Tsoffin shugabannin Afirka mata:

1993-4 - Sylvie Kinigi - mai rikon mukamin shugaban Burundi sanadin kisan Melchior Ndadaye

1996-7 - Ruth Perry - Shugabar majalisar kasa bayan yakin basasar farko

2006-18 - Ellen Johnson Sirleaf - an zabeta a matsayin shugabar Liberia

2009 - Rose Francine Rogombé - Shugabar Gabon ta rikon kwarya bayan mutuwar Omar Bongo

2012 - Monique Ohsan-Bellepeau - Mai rikon mukamin shugaban Mauritius bayan da Sir Anerood Jugnauth ya yi murabus

2012-14 - Joyce Banda - Shugabar Malawi bayan mutuwar Bingu wa Mutharika

2014-16 - Catherine Samba-Panza - Shugabar rikon kwarya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadda majalisar dokoki ta zaba

2015-18 - Ameenah Gurib-Fakim - Shugabar Mauritius da majalisar dokoki ta zaba

2018-present - Sahle-Work Zewde - Shugabar Ethiopia da majalisar dokoki ta zaba