BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: BBC

Sarakunan Larabawa da ke farautar tsuntsayen da ke ƙara ƙarfin maza

Wasu Larabawa na farautar tsuntsayen da ke ƙara ƙarfin maza Wasu Larabawa na farautar tsuntsayen da ke ƙara ƙarfin maza

A shekarar 1983, sojoji biyu suka tsaya wajen hayar mota da ke garin Pasni a gabar tekun kudu maso gabashin Pakistan.

Daya daga cikinsu ya tambayi mai wajen: "Kana da lafiyayyar mota? Za mu kai wani attajirin Balarabe Panjpur."

Mai wajen ya ce yana da ita, ya kuma hada su da dansa Hanif dominn ya nuna musu motar.

An yi hayar motar ne domin Yarima Suroor bin Mohammed al-Nahyan, daya daga cikin 'ya'ya shida na masarautar Hadaddiyar Daular Larabawa. Yana son zuwa Panjpur, mai nisan kilomita 100 daga wajen, domin farautar tsuntsun houbara bustards, da ba ko ina ake samu ba, da aka yi amanna namansa na karawa maza kuzari a lokacin jima'i.

Attajirin ya so motar, don haka ya karba a hannun Hanif a lokacin yana da shekara 31. Daga nan ne muka fara kulla dadaddiyar alaka, in ji Haji Hanif kamar yadda ake kiran shi a halin yanzu.

Shekaru 37 bayan nan, ya zamo daya daga cikin mai kula da tafiye-tafiyen masarautar zuwa Pakistan a kowacce shekara domin farautar tsuntsun houbaras.

Tsuntsun mai kunya, mai girman talo-talo na dab da karewa a ban kasa, don haka farautarshi na cike da ce-ce-ku-ce, amma duk da haka ana farautarsu.

Masu karfin fada a ji a Pakistan su ke bai wa masu farautar a asirce goyon baya, wanda aka yi gwamman shekaru ana yi, a wani bangare na yaukaka dangantaka tsakaninsu da attajiran Larabawan, wadanda ke kishirwar samun ayyuka da zuba jari.

Sai dai babu tabbacin gajiyar da Pakistan ke samu kan hakan, wadanda ke cikin harkar sun ce 'ya'yan sarautar na amfani da tafiyar ne domin shakatawa da jin dadi.

A watannin Nuwamba da Fabrairun kowacce shekara, Haji Hanif na karbar bakuncin 'yan gidan sarautar da ke zuwa farauta gundumar Balochistan, tafiyar awa daya daga garin Gwadar da ke gabar teku.

Da zarar karshen hunturu ya zo, an kammala farauta, ya gayyaci BBC domin ganin gagarumin shirin da ma'aikatansa ke tarbar bakin. Gagarumar liyafar da ake kashewa makudan kudade ana yi ne a Pasni, wurin da abubuwan da ake yi suke daurewa mazauna yankin kai na kashe kudi.

Mun hadu da maza biyu da suka kai mu kayataccen gidan Haji Hanif, mun bi ta hanya mai sauki zuwa farfajiyar gidan, babu nisa daga filin jirgin sama. Duka motocin an yi musu lambar Hadaddiyar Daular Larabawa, hakan zai sa mutane zaton muna daga cikin 'yan masarautar Abu Dhabi.

Wannan yanayin ya samo asali ne saboda yadda 'ya'yan masarautar Abu Dhabi ke yawan kai komo a yankin, musamman kan katon hoton shaho kamar yadda muke ganin da an shiga farfajiyar shiga gidan, duk da unguwa ce ta marasa galihu.

Ziyarar sarakunan ta sa mazauna yankin samun ayyukan yi. A lokacin da muka je gidan, mun ga mazaje na yi wa shaho hidima, wasu na gyara dakin dafa abinci, wasu kuma na sanya motocin alfarma samfurin SUV a cikin wani katon gareji.

Wani mutum sanye da kayan sarki ne ya yi mana jagora zuwa sashen masaukin baki, inda turare mai kamshin gaske ya yi mana maraba.

"Yaya wurin ya ba ku sha'awa?" in ji Haji Hanif, wanda ke zaune a daya daga cikin kujerun alfarmar da ke dakin.

Haji Hanif, mai shekara 60, ya zamo mai bayar da labarai kan abin da ya faru a baya. A lokacin da yake zagayawa da mu cikin kayataccen ginin ya shaida mana yadda ziyarar basaraken ta kasance a shekarun baya.

"Bayan mun sama masa motar, sai ya sake dawowa wajen mu. Kafin shekarar 1988 ni da mahaifina muna kula da motocin basaraken guda 20, saboda ya amince da mu."

Ga mazauna garin Pasni, ziyarar ta zame musu hanyar samun kudaden shiga, saboda ana daukar ma'aikata 35 wata guda gabannin lokacin ziyarar sarakunan.

Haka kuma ana samun mazan da ke kula da shahon, wadanda ke taimakawa wajen ba su horo. Sannan ana kai mazaje uku da ke aiki a lambun lemon zaki na sarakunan, da mutum guda mai yin wanki da guga.

Wasu na kula da dafa abinci da goge-goge, da masu kula da motoci. Sannan ana biyan wani mutum mai babur da zai dinga zuwa yana gano inda tsuntsayen houbara bustards suke, ta yadda ba sai sarakunan sun yi tafiya mai nisa ba lokacin farauta.

Su ma 'ya'yan Haji Hanif uku, an dauke su aiki domin taimaka wa mahaifinsu.

Babban dansa ne yake kula da garejin da aka ajiye motocin SUV 20 da sarakunan ke amfani da su, mai bi masa kuma yana aikin mai tsaron lafiyar sarakunan, sai na ukun yana tabbatar da ba a yi farautar tsuntsun ta barauniyar hanya ba ko sayar da shi a kasuwar bayan-fage.

A shekarar 1973 ne Pakistan ta fara gayyatar sarakunan bikin farautar. Tun daga lokacin rukuni daban-daban na sarakunan Larabawa suka fara kai ziyarar farautar tsuntsun houbara bustard, wanda yake yin balaguro zuwa kudu maso yammacin Balochistan a lokacin hunturu.

Zuwa shekarar 1989 gwamnatin yankin da ke samun goyon bayan hukumomi a Islamabad, ta sauya tsarin ta yadda ta bai wa sarakunan Larabawa daban-daban wuraren farauta.

An bai wa masarautar Abu Dhabi wuraren farauta a Pasni, Panjgur da Gwadar. Yayin da aka bai wa masarautar Qatar yankin Jhal Jhao da ke gundumar Awaran a gabashin gabar ruwa. An kuma bai wa masarautar Saudiyya yankin Chaghi, zuwa arewacinsa baki daya. Su kuma iyalai kamar na Haji Hanif da suke amintattun sarakunan alhakin kula da wuraren ya rataya a wuyansu, lokaci zuwa lokaci.

A shekarun 1970, masu farauta daga sassan kasashen Larabawa na kafa sansani a duk inda tsuntsun houbaras yake. Suna shafe kudan mako guda su na farauta, anan za adafa abinci,a kuma gasa naman tsuntsu a cinye kafin daga bisani su koma cikin gari.

Sai dai fargabar matsalar tsaro a yammacin Balochistan, inda mayakan jihadi ke kaddamar da hare-hare a 'yan shekarun nan, ta sa kafa sansani a daji na cike da hatsari. A yanzu yawancin sarakunan sun fi zama a manyan otal, ko kayatattun gidajen mutane kamar Haji Hanif. Daga nan ba sa yin tafiya mai nisa zuwa dajin da suke farauta wanda dama tuni ma'aikata sun gano inda suke.

Bisa al'ada shaho ne yake farautar tsuntsun houbaras mafi tsada - ana yanka wuyan tsuntsun da wuka da zarar an cafke shi. Mafarauta na kuma harbin tsuntsun. Amma a dan tsakanin nan masu safararsu, da masu kula da su na sakin tsuntsun ne domin shaho ya kamo su amma sai idan mafarautan suna kusa.

An dade ana ce-ce-ku-ce kan farautar houbara bustards, da aka fi sani da houbaras na yankin Asiya. Wanda a baya ya mamaye yankin Larabawa. Sai dai kungiyar kare gandun daji ta yi kiyasin a duniya baki daya nau'in tsuntsun 50,000 zuwa 100,000 ne suka rage wanda ke cikin tsuntsayen da ke fuskantar barazanar bacewa daga doron kasa.

Yawancin mutane a Pakistan ba su amince da abin da suka kira sukar iyayen gidansu ba, ga wasu na ganin wata hanya ce ta kulla alaka da manyan masu kudin yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar zuba jari da samar da ayyuka, da bai wa kasar bashi.

Tsohon mai magana da yawun ofishin harkokin wajen Pakistan ya ce sun yi kokarin kawo karshen abin kunyar, amma hakan ba ta samu ba. Ya kara da cewa: "alamu sun nuna akwai masu hannu a lamarin wadanda jami'an gwamnati ne da ba sa son kawo karshensa."

Wani tsohon jami'in Pakistan ya ce babu wani abin a zo a gani da aka samu game da dangantaka tsakanin kasashen biyu cikin shekaru 25.

A hunturun shekarar nan ma Pakistan ta sa ran zuwan Yariman da suke fatan balaguron farautar zai taimaka wajen gyara dangantakar da ta yi tsami tsakanin kasashen biyu. A shekarar da ta wuce Pakistan ta shiga jerin kasashen da 'yan kasashensu ba za su samu bizar shiga Hadaddiyar Daular Larabawa ba, wanda hanya ce ta samun kudaden shiga ga miliyoyin 'yan kasar.

Masu sharhi kan al'amura na ganin wannan wata hanya ce ta matsa wa Pakistan lamba, kan batutuwan da suka shafi Isra'ila, da rikicin yankin Kashmir. Sai dai firaiminista Imran Khan da mukarrabansa sun yi watsi da zargin.

Duk da haka, an ci gaba da farautar.

Ita ma Kotun Kolin Pakistan ta yi nasarar haramta farautar tun shekarar 2015, amma aka dage ta a shekarar 2016. Ko lokacin da dokar ke aiki, gwamnati ta ci gaba da bai wa sarakunan Larabawa wuraren farauta, amma tare da wasu sharuda.

Haji Hanif ya ce sarakunan na kyautata wa mutanen Pasni.

Yana cike da farin ciki ba wai saboda ayyukan yi da sarakunan suke samarwa ba, sun gina rijiyoyi da makarantu da asibitoci. Matsalar da makarantun ke fuskanta shi ne rashin malamai sannan asibitocin babu magunguna da ma'aikata.

"Sarakunan suna gina abu ne kawai, babu tabbacin samar da ma'aikata, wannan aikin gwamnatin yankin ne."

Duk da haka Haji Hanif baya son 'ya'yan shi su gaji aikin da yake yi.

"Ni boyi-boyin sarakunan ne, amma ba na fatan wani cikin 'ya'yana ya gaji aikin da nake yi. Su yi abin da ransu yake so, ko kasuwanci, su ma su samawa kansu mafita.

"Na shafe tsahon rayuwa ta ina wannan aikin, kuma ina son shi."