Mahukunta a Senegal sun dakatar da lasisin wasu gidajen talabijin guda biyu masu zaman kansu bayan da aka zarge su da mayar da hankali sosai kan zanga-zangar da ake ci gaba da yi yanzu haka a kasar sakamakon kame wani shugaban adawa.
Za a dakatar da Sen TV da Walf TV na awanni saba'in da biyu.
Tun da farko, 'yan sanda sun yi arangama da magoya bayan Ousmane Sonko a yankin kudancin Casamance, sannan rahotannin da ba a tabbatar da su ba na cewa an kashe mutum daya.
An kame Mista Sonko ne a ranar Laraba bayan an zarge shi da yi wa wata mata fyade a wani otel yayin da take yi masa tausa.
Ya bayyana lamarin a matsayin siyasa, da kuma kokarin abokan kawancen shugaban Macky Sall na tabbatar da cewa bai tsaya takara a zabe mai zuwa ba.
Tun da farko 'yan majalisa a kasar ta Senegal sun kada kuri'ar cire kariyar da fitaccen dan adawar wanda kuma dan majalisar dokokin kasar ne ke da ita, duk da ya musanta zargin da ake yi masa.
Shine mutumin da ya zo na uku a zaben shugaban kasa na shekarar 2019, kuma ana ganin shi a matsayin daya daga cikin yan takarar da ke da karfi a yankin Afirka ta Yamma, in ji kamfanin dillacin labarai na AFP.
Daya daga cikin jagororin adawa a ƙasar Pastef mai shekaru 46 ya zargi Shugaba Macky Sall, wanda ke wa'adin mulkinsa na biyu da musgunawa yan adawa, in ji AFP.
Masu aiko da rahotanni sun ce akwai yiwuwar labarin ya harzuka matasa magoya bayansa, wadanda suka yi zanga-zangar a watan da ya gabata lokacin da wani ma'aikacin gyaran kawata gashi ta shigar da karar fyade a kansa.