BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

Serie A: Inter za ta lashe kofin gasar Italiya na 19 jumulla

Kungiyar Inter na daf da lashin kofin Serie A Kungiyar Inter na daf da lashin kofin Serie A

Inter Milan na daf da lashe kofin Serie A na bana, bayan da ta doke Hellas Verona da ci 1-0 ranar Lahadi a wasan mako na 33.

Wannan ne karon farko da kungiyar wadda Antonio Conte ke jan ragama za ta lashe Serie A tun bayan 2010.

Inter da Milan kowacce tana da kofin Serie A 18 da ta lashe jumulla.

Tsohon dan wasan Manchester United, Matteo Darmian ne ya ci wa Inter kwallo a minti na 76 da hakan ya sa ta samu maki ukun da take bukata.

Da wannan sakamakon Inter ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin gasar Italiya da tazarar maki 13 tsakaninta da AC Milan ta biyu.

Ranar Litinin AC Milan za ta ziyarci Lazio a wasan mako na 33 da za su kece raini, kuma sauran wasa biyar - biyar kenan a karkare kakar bana.

Mai rike da kofi Juventus wadda ta ci tara a jere tana mataki na uku, bayan da ta tashi 1-1 da Fiorentina ranar ta Lahadi.

Dusan Vlahovic ne ya fara ci wa Fiorentina kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga, daga baya Alvaro Morata ya farke wa Juventus.