BBC Hausa of Wednesday, 17 March 2021

Source: BBC

Shawarwarin da Miyetti Allah ta bayar kan hare-haren da ake zargin Fulani na kai wa a Najeriya

Kungiyar Miyetti Allah ta ba da shawarwarin a wani taro a Yola a Adamawa Kungiyar Miyetti Allah ta ba da shawarwarin a wani taro a Yola a Adamawa

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta bayyana cewa matsalolin 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da ke faruwa a wasu jihohin Najeriya na ci mata tuwo a kwarya.

Kungiyar ta bayyana haka ne a wani taro da ta gudanar a Yola babban birnin jihar Adamawa.

Ta gudanar da taron ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zargin wasu Fulani makiyaya da hannu a satar mutane da kuma wasu matsalolin rashin tsaro a kasar.

Shugaban Miyetti Allah Kautal Hore, Abdullahi Bello Badejo, ya shaida wa BBC cewa kodayake ana zargin wasu Fulanin da hannu a kai hare-hare, amma sakacin da gwamnatoci daban-daban suka yi na shawo kan matsalolin da suka addabe su na cikin abubuwan da suka haifar da matsalolin d ake fama da su a yanzu.

A cewarsa: "Abin da ya shafi hrkar ilimi da batanci da ake yi wa Fulani kan sace-sacen mutane da fashi da makami, to mun lura cewa ba za mu zura ido ana yin irin wadannan abubuwa haka kawai ba.

Shi ya sa muka yi babban taro na kasa baki daya muka nemi wadanda suke da ilimi fitattu game da abin da ya shafi al'amura na Fulani, hada da fadakar da su da wayar da kansu a kan harkar ilimi da zamantakewa."

Abdullahi Bello Badejo ya kara da cewa cikin shawarwarin da kungiyarsu ta bayar har da "wajibi ne dai 'ya'ya a sa su a makaranta. Wadanda suke kiwo na harkar yawace-yawace da dabbobi a tafi kudu da sauransu, a dan saurara da wannan zuwa wani dan lokaci."

Ya ce sun yi la'akari da abin da zai taimaka wa Fulanin su gane cewa ana sane da su kuma za a dauki matakan inganta rayuwarsu.

Shugaban na Miyetti Allah ya ce sun rubuta takardu da za su gabatarwa gwamnatin tarayya da kuma gwamnatocin jihohi "game da yadda za a tanazar wa Fulani wurin zama."

Ya ce wasu daga cikin Fulani makiyayan da suka fandare ne suka fada harkar sace-sacen muane domin karbar kudin fansa, yana mai yin kira ga gwamnatoci su duba kalubalen da Fualni suke fuskanta domin su magance su.

'Yan Najeriya na da mabambantan ra'ayoyi game da yin sulhu da makiyayan da ake zargi da kai hare-hare kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Manyan mutane irin su fitaccen malamin addinin Musulunci Shiek Ahmad Gumi na ganin ya kamata gwamnati ta yi wa 'yan bindigar afuwa suna masu cewa hakan zai kawo karshen hare-haren da suke kai wa kan jama'a.

Sai dai a wata hira da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi da BBC Hausa ya shaida mana cewa ba da gaske 'yan bindigar suke ba domin kuwa sun sha cewa sun tuba amma su dawo su ci gaba da kai hare-hare.

Gwamnan ya ce yana da ra'ayin a buɗe wa 'yan bindigar wuta kuma babu batun sulhu tsakanin gwamnatinsa da masu garkuwa da mutane.

"Idan Gwamnatin Tarayya ba ta ba mu sojoji na sama da na ƙasa ba, an shiga dazukan nan an kashe 'yan ta'addan nan a lokaci ɗaya, to za mu ci gaba da zama cikin matsala," in ji El-Rufai.