BBC Hausa of Tuesday, 18 May 2021

Source: BBC

Sheikh Dahiru Bauchi ya amince da Sanusi a matsayin Khalifan Tijjaniya

Sheikh Dahiru Usman Bauchi (dama) tare da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II Sheikh Dahiru Usman Bauchi (dama) tare da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II

Babban malamin ɗarikar Tijjaniya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya amince da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, a matsayin Khalifa.

Shehin malamin ya amince da naɗin Sunusi lokacin da tsohon sarkin na Kano ya gabatar masa da takaddar tabbatar da naɗinsa a hukumance a matsayin Khalifan darikar Tijjaniyya a Najeriya a ziyarar da ya kai jihar Bauchi, kamar yadda ɗaya daga cikin ƴaƴansa ya tabbatar wa BBC.

A makon da ya gabata aka kawo ƙarshen saɓani da ke tattare da naɗin tsohon Sarkin na Kano, Muhammadu Sanusi II, a matsayin jagoran Darikar Tijjaniyya a Najeriya a hedkwatar ɗarikar ta duniya a Senegal.

Babban jagoran darikar, Mahi Nyass ne ya tabbatar da naɗinsa lokacin da ya karbi bakuncin tsohon sarkin a wata ziyarar watan azumin Ramadan da ya kai ƙasar.

An ambato Sheikh Dahiru Bauchi na cewa naɗin na Sanusi bai rusa jagorancin sauran shugabannin darikar Tijjaniyya ba, musamman waɗanda marigayi Shiekh Ibrahim Nyas ya naɗa.

Shehin malamin ya yi wa tsohon sarkin na Kano addu'ar jagoranci da kariya ga matsayin da aka ba shi.