BBC Hausa of Tuesday, 20 April 2021

Source: BBC

Shin sau nawa ana korar Mourinho daga aiki ne?

Tsohon kocin Tottenham Hotspurs, Jose Mourinho Tsohon kocin Tottenham Hotspurs, Jose Mourinho

Ranar Litinin Tottenham ta sanar da sallamar Jose Mourinho daga aikin kocin kungiyar, bayan wata 17 yana jan ragama.

Dan kasar Portugal ya maye gurbin Mauricio Pochettino a Tottenham a Nuwambar 2019, inda kungiyar ta kare a mataki na shida a Premier a bara.

A kakar bana kuwa kungiyar tana ta bakwai a teburin gasar Ingila, bayan da ta hada maki biyu daga karawa uku a Premier League.

A cikin watan Maris aka yi waje da Tottenham daga gasar Europa League karkashin jagorancin Mourinho.

Sai dai kuma kungiyar ta kai wasan karshe a Caraboa Cup da za ta fafata da Manchester City ranar 25 ga watan Afirilu.

Shin sau nawa aka kori Mourinho a kan aikin horar da tamauala.

Manchester United (2018/19)

Manchester United ta raba gari da Jose Mourinho cikin shekarar 2018 ranar Talata.

Hakan ya biyo bayan da United ta fara kakar 2018/19 da kafara hagu, inda ta ci wasa bakwai a fafatawa 19 a gasar Premier.

Daga lokacin United ta sallami Mourinho, duk da kungiyar tana ta biyu da tazarar maki 19 tsakaninta da ta daya a teburin Premier.

Ta kuma sallame shi ranar 18 ga watan Disambar 2018.

Chelsea (2007-2008)

Bayan da Mourinho ya lashe kofin Premier League biyu da League Cup biyu da FA Cup, Chelsea ta sallami kocin wanda a lokacin yake kaka ta hudu a yarjejeniya.

Mai shekara 55 bai goyi bayan da aka nada Abram Grant a matsayin daraktan kwallon kafar kungiyar ta Stamford Bridge ba.

An kuma kori kocin bayan da Chelsea ta sha kashi a hannun Aston Villa, sannan ta yi canjaras da Blackburn.

Sai kuma kunyiyar ta buga 1-1 da Rosenborg a Stamford Bridge a Champions League.

Real Madrid (2012-2013)

Mourinho ya kira kakar da cewar ita ce mafi muni a tarihinsa na horar da tamaula, bayan da Atletico ta yi nasara a kan Real Madrid ta lashe Copa del Rey.

Daga nan kuma sai dangantaka ta yi tsami tsakanin kocin da 'yan wasa, musamman Iker Casillas da kuma Sergio Ramos.

Tsohon kocin Inter Milan ya fada cewar 'yan jaridar Spaniya ba sa kaunarsa, kuma ya yi ta korafi kan ana fifita Barcelona a kan Real Madrid.

A karshen kakar Real Madrid ta sallami Mourinho.

Chelsea (2015-2016)

Chelsea ta kori Mourinho a karo na biyu, kuma wata bakwai kacal ya yi, duk da ci kofin Premier League da ya yi.

Kungiyar ta Stamford Bridge ta sallami kocin bayan da take ta 16 a teburin Premier League da tazarar maki daya tsakaninta da 'yan karshen teburi.

Mourinho ya zargi 'yan wasan Chelsea da juya masa baya, inda ya ce sun ci amanarsa.