Shugaban Amurka Joe Biden ya umarci hukumomin tattara bayanan sirri na kasar da su gudanar da bincike kan yadda kwayar cutar korona ta COVID-19 ta bayyana, yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce a kan asalin kwayar cutar.
A wata sanarwa Mista Biden ya umarci hukumomin da su rubanya kokarinsu a kan aikin sannan su ba shi rahoto cikin kwana 90.
Cutar koronar samfurin COVID-19 an fara gano ta ne a birnin Wuhan na China a karshe-karshen shekarar 2019. Kuma tun daga sannan ta addabi duniya da bazuwa kamar wutar daji, inda ta kama sama da mutane miliyan 168 wadanda aka tabbatar ke nan baya ga wadanda ba a gwada su balle a gano ta a jikinsu ba.
Sannan kuma an bayar da rahoton mutane akalla miliyan uku da rabi da ta kashe, kodayake alkaluman na karuwa.
Hukumomi dai sun danganta bayyanar kwayar cutar daga wata kasuwar sayar da naman ruwa a birnin Wuhan na China, kuma masana kimiyya sun yi amanna kwayar cutar ta fara yaduwa ne daga dabbobi zuwa mutane.
To amma rahotannin da ke fitowa daga kafafen yada labarai na Amurka a baya bayan nan na kara jaddada shedar zargin da aka taba yi a baya cewa, kwayar cutar ana ganin ta bayyana ne daga wani dakin binciken kimiyya a China.
Sai dai Chinar ta mayar da martani a kai, inda ta yi watsi, tare da sukar wadannan rahotanni, kana ta ce kwayar cutar kila daga wani dakin binciken kimiyyar ta bayyana amma a Amurka.
A sanarwar da ta fito daga fadar gwamnatin Amurka, Larabar nan, Shugaba Biden ya ce ya bukaci da a gudanar da bincike, a ba shi rahoto a kan asalin kwayar cutar ta korona samfurin Covid-19, tun bayan da ya hau mulki.
Rahoton kuma ya kunshi sanin ko kawayar cutar ta samo asali ne daga haduwar mutum da wata dabba da ke dauke da ita, ko kuma daga dakin binciken kimiyya ne ta fito bisa kuskure
Bayan da ya karbi rahoton ne a wannan wata, shugaban na Amurka ya bukaci da a kara zurfafa binciken.
Mista Biden a sanarwar ya ce, zuwa yau, hukumomin tattara bayanan sirri na Amurka sun yi gamayya a kan hanyoyi biyu da suke ganin kila ta nan ne aka samu bayyanar kwayar cutar, sai dai ba su cimma cikakkiyar matsaya a kai ba.
Shugaban ya ce matsayar hukumomin zuwa yanzu ita ce, yayin da bangare biyu nasu ya karkata ga zargin farko na cewa kwayar cutar ta yadu ne daga wata dabba zuwa mutum.
Bangare daya kuwa ya karkata ne ga daya fahimtar ta cewa daga dakin kimiyya aka saki kwayar cutar.
Amma kuma ya kara da cewa dukkanin bangarorin ba su hakkake matsayar tasu ba - ya kara da cewa yawancin masu binciken na hukumomin suna ganin babu wata sheda isasshiya da za ta sa a fi yarda da daya daga cikin fahimtar biyu.
A don haka ne Shugaban na Amurka ya bukaci hukumomin da su rubanya kokarinsu, su tattara tare da nazarin bayanan da za su sa a kai ga kusa da samun tabbatacciyar matsaya kan asalin kwayar cutar ta korona (Covid-19).
Kuma su ba shi rahoto nan da kwana casa'in, amma kumu hukumomin su tabbatar da majalisar dokokin kasar na sane sosai da aikin da suke yi.
Ya kammala bayanin nasa da cewa Amurka za ta ci gaba da aiki tare da abokan burminta a fadin duniya domin matsa wa China ta shiga sosai a dama da ita wajen gudanar da bincike na duniya na gaskiya ba tare da wata rufa-rufa ba, ta kuma bayar da dama ga samun duk wasu bayanai da sheda da za a bukata.
A watan Maris na wannan shekara, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar da wani rahoto da ta rubuta da hadin guiwar masana kimiyya na China a kan asalin kwayar cutar ta korona nau'in Covid-19, inda a ciki suka ce batun fitar da kwayar cutar daga dakin kimiyya abu ne mai wuyar gaske.
Amma kuma hukumar ta WHO ta yarda cewa akwai bukatar kara zurfafa bincike.
Sai dai an ci gaba da nuna shakku da tambayoyi, kuma wasu rahotanni da aka danganta ga hukumomin tattara bayanan sirri na Amurka sun ce an kwantar da wasu kwararru uku na cibiyar bincike kan kwayoyin cuta ta birnin Wuhan na China a asibiti a watan Nuwamba na 2019.
Wato Makwanni da dama kafin China ta yarda ta bayyana mutum na farko da ya kamu da sabuwar cutar a birnin.