BBC Hausa of Friday, 4 June 2021

Source: BBC

Simone Inzaghi: Inter Milan ta sanar da kocin da ya maye gurbin Antonio Conte

Simone Inzaghi, sabon kocin Inter Milan Simone Inzaghi, sabon kocin Inter Milan

Inter Milan ta nada Simone Inzaghi a matakin sabon kocinta, domin maye gurbin Antonio Conte a kungiyar.

Mai shekara 45, ya koma Inter wadda ta lashe Serie A na bana kan yarjejeniyar kaka biyu, ya kuma kawo karshen alaka da Lazio, bayan shekara 22.

Inzaghi wanda ya lashe Coppa Italiya da kuma Italian Super Cup biyu a Lazio, ya kai kungiyar mataki na shida a kakar Serie A da aka kammala.

A matsayinsa na dan kwallon ya lashe kyautuka da yawa a lokacin da ya taka leda a Rome ciki har da cin Serie A.

Inzaghi wanda kani ne ga tsohon dan kwallon Juventus da AC Milan, Filippo ya kai Lazio zagaye na biyu a Champions League a 2020/21, karon farko da ta buga gasar bayan shekara 13.

Sai dai kuma za a so kocin ya kara kokari ganin rawar da Conte ya taka a kungiyar da matakin da ya kai Inter a fannin kwallon kafa a Italiya da Turai da duniya.

Conte wanda ya yi kaka biyu a Inter ya kai kungiyar Europa League ya kuma yi na biyu biye da Juventus wadda ta lashe Serie A na bara a kakar farko.

A kaka ta biyu kuwa ya lashe kofin ya kuma yi wa Juventus burki, bayan da ta ci Serie A tara a jere, kuma Juve ta karkare kakar tamaular Italiya a mataki na hudu.

Inzaghi ya koma aikin horar da tamaula, bayan da ya yi ritaya daga taka leda a 2010.

Ya kuma fara jan ragamar matasan Lazio daga baya ya karbi aikin rikon kwaryar babbar kungiyar, sannan aka nada shi koci a 2016.