Jami'an tsaro sun kashe gomman mutane a Myanmar wanda shi ne mafi muni tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki a watan daya gabata.
Wata kungiya da ake kira AAPP ta ce an halaka mutum 91 ciki har da yara kanana.
"Suna ta kashemu kamar tsuntsaye ko kaji, har a cikin gidajenmu", a cewar wani mazaunin garin Myingyan.
"Za mu ci gaba da zanga-zangar".
Wata kafar watsa labarai ta cikin gida ta ce adadin wadanda suka halaka ya kai 114.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta samu rahotanni da ke cewa an kashe gomman mutane tare da raunata daruruwa a wurare 40.
Sojojin sun yi amfani da karfi ne bayan da masu zanga zanga suka bijirewa gargadin da aka yi mu su inda suka hau tituna a ranar tunawa da mazan jiya.
Amurka da Burtaniya da Tarayyar Turai sun yi Allah wadai da tashin hankalin.
Mace-macen baya-baya nan sun sa adadin wadanda suka halaka tun bayan da aka soma zanga zangar ya zarce 400 tun daga ranar 1 ga watan Fabarairu.
Sojoji sun yi juyin mulki ne bayan zaben da ya bayyana cewa jam'iyyar NLD ta Aung San Suu Kyi ta yi nasara.