Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kubutar da mutane 10 da aka sace kusan makwanni biyu da suka gabata a gidajen ma'aikatan Hukumar Kula da Filin Jirgin Sama ta Tarayya (FAAN) da ke karamar Hukumar Ikara.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar, Samuel Aruwan, ya ce a ranar Laraba ne sojojin na Najeriya suka ceto mutane 10.
Mista Aruwan, wanda ya yi wa yan jarida bayani game da ci gaban da aka samu a fannin tsaro na jihar, ya ce ba za a iya bayar da cikakken bayani game da wurin da aka kubatar da mutanen ba saboda dalilan tsaro.
A ranar juma'ar da ta gabata ne yan bindiga suka kai hari bayan da suka fasa katangar rukunin gidajen inda suka awon gaba da mutun 10 .
Bayan wannan hari ne yan bindigar suka shiga cikin kwalejin gandun daji da ke kusa da Mando inda suka yi awon gaba da mutum sama da talatin.