BBC Hausa of Thursday, 15 April 2021

Source: BBC

Somaliland da Taiwan: Ƙasashen da ba su da ƙawaye da yawa amma sun shiga hancin China

Somaliland ta bude ofishinta a Taiwan a watan Satumbar shekara da ta wuce Somaliland ta bude ofishinta a Taiwan a watan Satumbar shekara da ta wuce

Duka Taiwan da Somaliland yankuna ne da cikin alfahari suka ayyana cin gashin kan su amma kuma babu wacce har yanzu kasashen duniya suka san da zaman ta a kan haka., kuma yanzu da Mary Harper ke bayar da rahoto suna kara nausawa kusa da juna.

"Barka da zuwa wannan ofishinmu mai mutumtawa,'' in ji Chou Shuo-Wei Amir, jami'in ofishin huddar jakadancin Taiwan a yankin Somaliland.

Ofishin na cikin wani katafaren gini a kusa da ma'aikatar harkokin addini a Hargeisa babban birnin yanki na Somaliland.

Tutar Taiwan tana kadawa a hankali a cikin wani yanayin iska mai dadi da ke kadawa - mai launin ja, da fari da shudi ce da ke kara haskawa a kan launin shudi na sararin sama.

Duk da cewa wasu na kallon dangantakar a matsayin wani abin mamaki, yankunan Somaliland da Taiwan na da wata irin dangantakar ƙut-da-ƙut.

Ɓata wa kasashen China da Somalia rai

Dukkanninsu biyu kasashen duniya ba su san da zamansu ba kana duka suna da manyan makwabta - Somalia da China - da suka dage a kan cewa yankunansu ne.

A shekarar da ta gabata ne Somaliland da Taiwan suka kulla dangatakar huldar diflomasiyya da makwabtansu ke nuna bacin rai a kai.

Somalia ta yi Allah-wadai da Taiwan kan ƙawancenta da Somaliland. Mahukuntan kasar China sun je yankin na Somaliland ta kuma umarce ta da ta yanke huldar dangantaka da Taiwan.

Akwai yiwuwar kasar China na kallon dangantakar Taiwan da Somaliland a matsayin mai kawo wani cikas kan shirinta na gina hanyoyin zirga-zirgar kasuwancin teku da na kasa a fadin yankunan Asia, da Gabas ta Tsakiya da Afirka.

Yankin Somaliland mai tashar jiragen ruwa ta Berbera, ka iya toshe mashigin ruwanta na Maritime Silk da ke kan gabar ruwan Afirka.

Me yiwuwa kuma kasar China ta rika sa ido kan dangantakar Somaliland da Taiwan cikin fargaba kadan saboda ta kafa sansanin sojinta na kasashen waje na farko a makwabciyar ta kasar Djibouti.

Taiwan na kallon Somaliland a matsayin wani matakin farko a burin da ta ke da shi a yankin.

"Somaliland wata hanya ce ga Taiwan zuwa yankin Gabashin Afirka,'' in ji wakilin kasar Taiwan a Somaliland, Allen Chenhwa Lou, zaune a karshin hoton shugaban kasar shi Tsai Ing-wen.

"Daga nan ina wakiltar Taiwan a kasashen yankin Gabashin Afirka 10, da suka hada da Kenya da Ethiopia."

Somaliland daya daga cikin yankuna biyu na Afirka ne da ke da cikakkiyar dangantakar huldar diflomasiyya da Taiwan.

'Babbar aminiyar Somaliland'

Mr Lou ya bayyana dangantakar da ke tsakain yankunan biyu a matsayin ''ko wacce za ta samu ribarta ciki''.

Taiwan na bayar da tallafi a bangaren ayyukan gona, da fasahar zamani, da ilimi, da harkokin kiwon lafiya, da zaɓuɓɓuka da kuma makamashi. Somaliland na da wurare masu amfani, arzikin wuraren kamun kifi, da arzikin kasa, da kuma harkokin yawon bude ido.

"Somaliland na kiran Taiwan a matsayin 'babbar aminiyarta," in ji Mr Lou. "Amma na gwammace in ga dangantakarmu ta kasance ta hadin kai da morar juna. Za mu kasance da Somaliland a ko da yaushe.

"Ba ma bukatar neman wani 'yanci yanzu saboda tuni muka riga muka ayyana kanmu a matsayin masu cin gashin kanmu.

''Abin da muke bukata kawai shi ne a san da zamanmu. Dukannninmu muna fama da wannan mawuyacin hali."

Somaliland da Somalia

  • Wacce Turawa suka rike ta shiga cikin kasar Somalia a ranar 1 ga watan Yuli shekarar 1960


  • Ta ayyana kasancewa mai cin gashin kanta bayan hambare shugaban mulkin soja na Somalia Siad Barre a shekarar 1991


  • Hakan na zuwa ne bayan tashin hankalin da dubban darururwan mutane suka mutu kuma suka tashi garuruwa


  • Somaliland na da tsarin siyasa, da ma'aikatun gwamnati, da rundunar 'yan sanda da kuma kudadenta.


  • Amma ba kowa ne a yankin Somaliland yake jin dadin sabuwar dangantakar ba, kuma ko rasa kasar China a matsayin aminiya wani abu ne da ya dace.

    "Mutane biyu da ke cikin matsala ba za su iya taimakon juna ba,'' in ji wani mai sayar da dabbobi Ismail Mohamed.

    "Muna bukatar babbar kasa China fiye da yadda muke bukatar karamin yanki Taiwan."

    Wata 'yar kasuwa Muna Aden ita ma tana dari-dari da lamarin.

    "Dangantaka da Taiwan na nuni da wautar 'yan yankin Somaliland," in ji ta.

    "Mun dauka Somaliland ta nemi zawarcin Taiwan ne a matsayin wata hanya ta jan hakalin kasar China wajen cewa ''Muddin ba ki aure mu ba, za mu auri dayan''. Ba mu taba zaton za su kulla wannan dangantaka ba.

    "Babban kuskure ne da kasar China ba za ta taba mantawa da shi ba."

    Amma mahukunta a yankin Somaliland ba ya bayar da kansa ba ne. Mukaddashin ministan harkokin waje Liban Yousuf Osman, ya kare dangantakar yana cewa yankunan biyu na da abubuwa biyu iri daya - dimkoradiyya da kuma 'yanci.

    "Muna maraba da duk kasar da ke bukatar kulla dangantaka da Somaliland da suka hada da China. Amma ba za mu kori Taiwan saboda kasar China ba.''

    Taiwan da China

  • China da Taiwan sun kasance masu gwamnatoci daban-daban tun bayan yakin basasar kasar China a shekarar 1949


  • An samu karuwar tashin-tashina a shekarun baya kuma Beijing ba ta yanke kauna daga amfani da karfin soji wajen sake kwato tsibirin ba


  • Duk da cewa kasashe kadan ne suka san da zamanTaiwan a hukumance, zababbiyar gwamnatinta na da alaka mai karfi ta kasuwanci da kasashe da dama.


  • Mr Osman na da kyakkyawan fata ga Somaliland. "Za mu iya zama Taiwan din yankin Gabashin Afirka. Taiwan na da ɗumbin nasarori don haka muna son mu yi koyi da ita ta fuskar bunkasa."

    Ya bayyana yadda kasashe da dama ke kafa ofisoshi a Hargeisa babban birnin yankin, da suka hada daTurkiyya, da Ethiopia, da Djibouti, da Kungiyar Tarayyar Turai, da Birtaniya, da Amurka, da Hadaddiyar Daukar Larabawa.

    Kamar Taiwan, akwai wasu yankunan da ba su san da zamansu ba da ke sha'wara kulla dangantaka da Somaliland.

    A shekarar 2020, wakilan kasashen Birtaniya, da Daular Yellow Mountain, wani yanki da ke tsakanin kasashen Masar da Sudan, ya ziyarci Hargeisa cike da fatan bude ofishin huddar jakadanci a can.

    A nata bangaren, Somaliland ta bude ofishin hulɗar jakadancinta a Taiwan, karkashin jagorancin Mohamed Hagi.

    "Ina matukar jin dadin zama a Taipei," ya ce.

    "Yanayin mai kyau da dadi ne kana mutanen suna da wayewar kai. Suna son su san abubuwa game da Afirka daga gaare mu.''

    "Sai ina yi musu bayani cewa Somaliland ba Somalia ba ce, da kawai suke dangantawa da 'yan fashin teku da 'yan ta'adda.''

    Mr Hagi ya ce, abin da ya sani shi ne, 'yan Somaliland uku ne kawai a Taiwan - shi da sauran mutane biyu da ke aiki tare da shi.

    Amma yana sa ran karin wasu mutane nan ba da dadewa ba, bayan da Taiwan ta bai wa daliban Somaliland 20 tallafin karatu, kuma akwai yiwuwar kwararar 'yan kasuwa bayan da dangantakar tattalin arzikin ta kara bunkasa.

    Wakilin Taiwan a Somaliland Mr Lou ya ce, lokacin da ya isa yankin a shekarar 2020 ya dan samu damuwa game da al'adu, kuma shi ne karon farko da ya taba zuwa Afirka. Bai samu abubuwan da ya saba samu ba a kasashen da ya taba aiki, amma ya koyi yadda zai ji dadin zama ''saukin kai da kuma addini'' na rayuwa a Somaliland.