Kungiyar Tottenham ta tuntubi tsohon kocinta, Mauricio Pochettino kan idan zai sake komawa aiki a karo na biyu.
An kori kocin mai shekara 49 daga Tottenham cikin Nuwambar 2019, bayan shekara biyar da ya ja ragamar kungiyar.
Pochettino dan kasar Argentina ya karbi aikin horar da Paris St Germain a watan Janairun 2021.
Sai dai kuma PSG ta kasa cin Ligue 1 a bana kuma karo na biyu a kaka tara kenan, ta kuma yi rashin nasara a hannun Manchester City a Champions League a wasan daf da karshe.
A watan jiya ne Tottenham ta kori Jose Mourinho, wanda ya maye gurbin Pochettino a kungiyar.
Daga nan ne ta nada kocin matasanta, Ryan Mason a matakin rikon kwarya zuwa karshen kakar nan, inda kungiyar ta kasa daukar Caraboa Cup, wanda Manchester City ta yi nasara.
Haka kuma Tottenham ta karkare kakar bana a mataki na bakwai a gasar Premier League ta bana.
BBC ta fahimci cewar ba batun tuntuba tsakanin Tottenham da PSG, wdda ta gana da Pochettino kan tsare-tsaren tunkarar kakar badi.
Pochettino ya kai Tottenham wasan karshe a Champions League a 2019, wanda Liverpool ta lashe.
Tottenham ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Chelsea a League Cup a 2016, sannan ta yi ta biyu a Premier League, wanda Chelsea ta lashe a 2016/17.