Tsohon yerima mai jiran gadon masauratar Jordan, ya ce an yi masa daurin talala karkashin samamen da ake kai wa masu adawa da gwamnati.
A wani hoton bidiyo da lauyansa ya aikewa BBC, yerima Hamzah bin Hussein, wanda kani ne ga Sarki Abdullah amma dakinsu ba daya ba, ya zargi shugabannin kasar da Almundahana, da rashin tabuka wani abin a zo a gani da tozartarwa.
Wannan na zuwa ne bayan kamen da aka yi wa wasu manya da ake zargin suna da alaka da juyin mulkin sojoji.
Tun farko rundunar sojin kasar ta musanta cewa an yi wa yerima Hamzah daurin talala.
Sai dai ta ce an umarce shi a kan ya daina yin abubuwa da za su kawo cikas ga tsaron kasa da zaman lafiya.
Matakin na zuwa ne bayan ziyarar da yeriman ya kai zuwa wasu shugabannin kabilu.
Jordan babbar kawace ga Amurka wadda ke taimaka wa sojojin Amurka a ayyukan tsaro.
Haka kuma ta na cikin kawancen da Amurka take jagoranta a fadan da take yi da mayakan IS.
Kasar ba ta da albarkatun kasa sosai kuma tattalin arzikinta ya fuskanci matukar koma baya sanadin annobar korona.