BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021

Source: BBC

Tuchel ya yi wasa 11 a jere ba a doke shi ba a Chelsea

Kocin Chelsea Thomas Tuchel Kocin Chelsea Thomas Tuchel

Chelsea ta yi nasarar doke Everton da ci 2-0 a wasan mako na 27 a gasar Premier League da suka kara a Stamford Bridge ranar Litinin.

Chelsea ta fara cin kwallo ta hannun Ben Godfrey da ya ci gida a minti na 31 da fara take leda, sannan Jorginho ya ci na biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Da wannan sakamakon Chelsea ta ci gaba da zama ta hudu a kan teburin Premier da maki 50, ita kuwa Everton tana ta biyar mai maki 46.

Wannan kuma shi ne wasa na 11 da kocin Chelsea, Thomas Tuchel ya ja ragamar kungiyar da kawo yanzu ba a yi nasara a kansa ba.

Tuchel ya karbi aiki a hannun Frank Lampard ranar 26 ga watan Janairu, ya kuma fara jan ragama 27 ga watan Janairu a karawar da ya tashi 0-0 da Wolverhampton a gasar Premier League.

Cikin wasanni 11 a jere da kocin ya ja ragamar Chelsea ya yi canjaras uku a wasa da Southampton da Manchester United da wanda ya fara da Wolverhamopton.

Ya kuma ci Barnsley 1-0 a FA Cup ranar 11 ga watan Fabrairu da yin nasara a kan Atletico Madrid da ci 1-0 a Champions League ranar 23 ga watan Fabrairu.

Sauran wasa shida a Premier League ya ja ragama wasannin, kawo yanzu an ci Chelsea kwallo 2, ita kuwa ta zura 13 a raga a wasa 11 da Tuchel ya yi.

Ranar 13 ga watan Maris Chelsea za ta buga wasan Premier League da Leeds United, sannan ta karbi bakuncin Atletico Madrid a wasa na biyu a Champions League ranar 17 ga watan Maris.