BBC Hausa of Thursday, 3 June 2021

Source: BBC

Twitter ya ce ya goge sakon Shugaba Buhari saboda 'karya ƙa’ida'

Sakon Buhari da Twitter ta goge Sakon Buhari da Twitter ta goge

Kamfanin Twitter ya goge ɗaya daga cikin jerin saƙwannin da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa a ranar Talata.

Twitter ya goge inda shugaban ya ce "matasan yanzu ba su san girman ɓarna da hasarar rayukan da aka yi ba a yaƙin basasa ba. Mu da muka shafe wata 30 a fagen daga, muka ga bala'in yaƙin, za mu bi da su da salon da suka fi ganewa," in ji Buhari.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a yayin da yake ganawa da shugaban Hukumar Zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta INEC ranar Talata a fadarsa da ke Abuja.

Daga baya ne kuma Twitter ya goge sakon daga shafin shugaban na Najeriya.

Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar wa BBC da cewa tana sane da matakin da Twitter ya ɗauka, amma kuma ta aika da buƙatar neman jin dalilin da ya sa kamfanin ya goge saƙon.

Me ya sa Twitter ya goge saƙon?

Kamfanin na sada zumunta ya ce saƙon ya saɓa sharuɗɗansa.

Amma taƙamaimai kamfanin na Twitter bai bayyana ɗaya daga cikin sharuɗɗansa da saƙon na Buhari ya saɓa ba, amma yana tura mutane zuwa ga shafinsa na ƙa'idojinsa da kuma dalilin da zai sa ya goge duk wani saƙo.

Ƙa'idojin sun ce "idan har muka gano saƙo ya saɓa ƙa'idojin Twitter, za mu tambayi wanda ya saɓa dokar ya cire shi kafin ya iya aika wani saƙo."

Za mu tura sakon sanarwa ta imel ga mai shafin tare da tantance saƙon da ya saɓa sharuɗɗan.

Mene ne sharuɗɗan Twitter?

Ka'idojin kamfanin Twitter suna adawa da duk wani saƙo da ke goyon bayan rikici.

"Sharuɗɗan sun shafi tabbatar da ko wane mutum zai iya mu'amula ba tare da wata fargaba ba."

"Ba za ka iya yin barazana ga wani ba ko wata ƙungiya ba. Kuma ba za mu amince da duk wata da'awa da murnar rikici ba, in ji Twitter.

Ba wannan ne karon farko da kamfanin na sada zumunta ya ɗauki mataki kan wani sakon shugaba ba.

A watan Janairu, kamfanin ya taɓa goge saƙon shugaban Amurka, Donald Trump kan zarginsa da ƴaɗa fitina, kafin su haramta shafin na tsohon shugaban baki ɗaya.

Me gwamnatin Buhari ta ce?

Gwamnatin Buhari ta zargi Twitter na nuna son kai bayan goge ɗaya daga cikin saƙon Shugaba Muhammadu Buhari.

Ministan yaɗa labaran Najeriya Lai Mohammed, ya shaida wa manema labarai cewa "Twitter ya yi biris da saƙwannin nuna ƙiyayya da ƙungiyar IPOB ke yaɗawa amma kuma ta yi gaggawar ɗaukar mataki kan saƙon shugaba."

Ministan ya ce yana mamakin yadda za a ce shugaba ba zai bayyana damuwarsa ba kan wata ƙungiya da ke ba mambobinta umarni su kai hari ofisoshin ƴan sanda da kashe ƴan sanda.

"Twitter yana da nasa dokoki, amma ba dokar duniya ba ce," a cewar Lai Mohammed.

Sharhin Barista Bulama Bukarti

Kalaman na Shugaba Buhari sun haifar da mahawara inda ƴan Najeriya da dama kowa da yadda ya dauki kalaman, musamman yadda ya yi magana da kakkausar muryar da amo irin na ma'abota iko, yana gargaɗi ga masu kai hare-hare kan kaɗarorin gwamnati da jami'an tsaro.

Masana sha'anin tsaro a Najeriya kamar irinsu Barista Bulama Bukarti da ke gudanar da bincike a kan harkokin tsaro a nahiyar Afirka na ganin cewa babu laifi a cikin kalaman na shugaba Buhari.

Amma ya ce akwai bukatar shugaban ya dinga murza-gashin-baki tare da ɗaga murya a duk lokacin da ya dace, inda ya ce yawan shirun da yake yi ne ya sa wasu ke cewa kamar babu shugabanci a kasar.

Wasu ƴan Najeriya kuma sun kushe kalaman shugaban kasar ne suna zargin cewa ya fito ɓaro-ɓaro ya nuna ba ya tare da wani ɓangaren al'ummomin kasar, musamman ƴan ƙabilar Igbo.

A cewar su, bai yi irin wannan zare ido ba a kan hare-haren da ƴan Boko Haram da masu satar mutane a ke yi a arewacin Najeriya ba.