BBC Hausa of Thursday, 1 April 2021

Source: BBC

Uefa na nazarin ƙara yawan ƴan wasa da za su buga gasar Euro

Hoton yan kwallon Ingila Hoton yan kwallon Ingila

Uefa na nazarin ko ta amince a ƙara yawan ƴan wasa fiye da 23 a gasar cin kofin nahiyar Turai.

An taɓo batun ne a taron kwamitin zartarwar hukumar a ranar Laraba.

Wannan na zuwa bayan hukumar ta amince da yawan ƴan wasan da kungiya za ta iya canza wa a wasa zuwa biyar.

Yayin da cutar korona ke ƙara bazuwa a Turai, wasu masu horar da ƴan wasa na ganin ƙara yawan tawaga zai magance ƙalubalen da za a iya fuskanta idan har wani ɗan wasa ya kamu da cutar, maimakon ɗage wasan baki ɗaya.

Zuwa yanzu Uefa ba ta yanke shawara game da batun, kuma ba a fayyace cewa ko ƴan wasan da za a ƙara za su kasance na wuccin gadi ba ko kuma za su kasance a matsayin za a iya saka su a wasa.

Wannan wani ruɗani ne da ya kamata a yanke shawara akai.

Zuwa makon gobe hukumar ƙwallon Turai take sa ran karɓar matakai da aka ɗauka daga filayen da za su karɓi baƙuncin wasannin.

Wannan zai bayar da damar yanke shawarar ko za a ci gaba da shirin da aka yi ko kuma dole sai an soke wasu filayen da aka tsara a za gudanar da wasannin.