BBC Hausa of Tuesday, 23 March 2021

Source: BBC

Ugo Ugochukwu: Ba'amurke dan asalin Najeriya da McLaren ya dauka domin yi masa tseren Formula 1

Ugo Ugochukwu Ugo Ugochukwu

Tawagar tseren motoci ta McLaren ta rattaba hannu kan kwantiragi da Ugo Ugochukwu mai shekara 13 domin taimaka masa waje yin gasar tsren motoci ta Formula 1 a rukunin yara.

Tawagar McLaren ta ce yarjejeniyar ta ba su damar kulla wata yarjejeniyar da Ugochukwu a tseren motoci nan gaba.

Shugaban McLaren Zak Brown ya ce sun dade suna kallon yadda yaron yake samun ci gaba a wannan fannin.

"Domin haka da dama ta samu ba mu bata lokaci ba wajen rattaba hannu kan kwantiragin," inji Brown.

Wannan mataki ya bai wa McLaren damar da suka kira mai tagomashi, suna da damar ci gaba da rike Ugo domin yin tseren mota a Formula 1 nan gaba, akwai kuma damar yin hakan ga wasu kamfanonin idan suna da bukata.

Shi ma McLaren, kamar sauran 'yan tawagar Formula 1, suna da shirin horas da matasan direbobi na tsawo wasu shekaru.

Cikin dalibansu akwai shahararren dan tseren Formula 1 wato Lewis Hamilton wanda shi ma suka sanya hannu da shi a lokacin yana da shekaru 13 kamar dai Ugo.

Kuma har yanzu yana tare da su inda a halin yanzu shi ne zakara cikin direbobin F1 da ake yi wa lakabi da black driver.

Tun shekarar 2015 rabon da F1 ta samu direba Ba'amurke, bayan Alexander Rossi da ya shiga tseren mota 5 a jere tare da tawagar Marussia a shekarar.

Ba'amurke na karshe da ya yi nasara a Grand Prix a shekarar 1978 shi ne zakaran duniya Mario Andretti.

Shugaban masu horas da tawagar McLaren ta F1 Andreas Seidl ya ce: "Ugo hazikin yaro ne da muke ganin tauraruwarsa za ta haskaka nan gaba.

"Duk da cewa yanzu ya soma, amma a bayyane take za a yi fasihin dan wasa nan gaba. Wannan hannun da muka rattaba na nuna yadda muke kokarin zakulo sabbin yara masu basira a fagen wasanni da tallafa musu domin a ci gajiyarsu nan," in ji shi.

Shi kuwa Ugochukwu cewa ya yi: "Sanya hannu da babban kamfanin tseren mota kamar Mclauren abin alfahari ne, hakika karramawa ce. Tallafin McLaren yana da muhimmanci, kuma zai taimaka wa yara matasa cimma burinsu na zama fitattun 'yan tseren mota. A halin yanzu zan mayar da hankali kan koyon tuki, wanda McLaren za su taimaka min ta fannoni da."

Abin da ya kamata ku sani kan Ugo

An haifi Ugochukwu a birnin New York, amma kuma mahaifiyarsa 'yan Najeriya ce, mai suna Oluchi Onweagba-Orlandi mai tallan kayan kawa da ta yi aiki da manyan kamfanoni kamar su Gucci, Fendi, Chanel, Christian Dior da sauransu.

Oluchi, wadda ta girma a birnin Lagos na Najeriya, ta fara sana'ar kayan kawa a shekarar 1998 inda ta lashe kyautar 'Face of Africa' a shekarar.

Ta bayyana jin dadinta a shafinta na Instagram kan wannan nasara da danta ya samu.