BBC Hausa of Friday, 4 June 2021

Source: BBC

United Africa Republic - Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan sauya wa kasar suna zuwa UAR

Shawarar sake sunan kasa ya ja cheche ku che a shafukan sada zumunta Shawarar sake sunan kasa ya ja cheche ku che a shafukan sada zumunta

A yayin da ake zaman jin ra'ayoyin 'yan Najeriya kan sauya kundin tsarin mulkin 1999, ana ta yada rahotannin cewa an gabatar wa majalisar wakilai bukatar a sauya sunan kasar zuwa "United Africa Republic".

Rahotanni sun ce daga cikin 'yan Najeriyar masu bayyana ra'ayoyinsu a zauren majalisar ne wani ya gabatar da wannan bukata.

Sai dai wannan kudurin na bukatar amincewa kafin a kai ga tabbatar da sabon sunan. Akwai kasashen Afirka da dama da suka sauya sunayensu a bisa wasu dalilai.

Wannan labari shi ne ya fi jan hankalin 'yan kasar a ranar Alhamis musamman matasa a shafukan sada zumunta da muhawara.

Maudu'in United African Republic da aka kaddamar a Tuwita shi ne na biyar mafi tashe inda aka yi amfani da shi fiye da sau 70,000 zuwa karfe uku na yammacin ranar.

Mutane sun yi ta bayyana ra'ayoyi daban-daban inda wasu suka mayar da abin raha, wasu kuma suka nuna hakan ci gaba ne mai kyau.

Sai dai wasu na ganin hakan ba abu ne mai muhimmanci ba don ba sauya suna ne matsalar Najeriya ba a yanzu.

Wasu har sun fara sanya hotunan kudi na raha da sabon sunan na United Africa Republic.

Me mutane ke cewa?

@kvng_rhamzy ta ce: "Saboda kasashe irin su United States (Amurka) da United Kingdom (Birtaniya) da United Arab Emirates (Hadaddiyar Daular Larabawa) sun ci gaba ne shi ya sa wasu ke son a sauya wa Najeriya suna zuwa UNITED AFRICAN REPUBLIC?